Hatsarin Jirgi Ya Rutsa da Mutanen da Suka Gudo daga Harin Yan Bindiga, An Rasa Rayuka
- Jirgin ruwa da ya dauko mutanen da suka gudu daga harin yan bindiga ya nutse a yankin karamar hukumar Sabon Birni a Sakkwato
- Rahoto ya nuna cewa ana fargabar mutane da dama sun mutu a hatsrin wanda ya auku ranar Alhamis da ta gabata
- Mazauna yankin sun shaida wa Legit Hausa yadda suke fama da yawan hadurran jiragen ruwa, wanda ke jawo asarar rayuka da
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Sokoto - Rahotanni sun nuna cewa an sake samun hatsarin jirgin ruwa mai muni a jihar Sakkwato da ke Arewacin Najeriya.
An tattaro cewa jirgin, wanda ya dauko mata da yara ya yi hatsari ne sakamakon bugun bakin gada ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025.

Source: Original
An kara samun hatsarin jirgi a Sakkwato
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jirgin ruwan ya dauko fasinjoji, wadanda mafi yawancinsu mata ne da suka gudo daga harin yan bindiga, lokacin da ya kife.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana fargabar dai fasinjoji da dama sun mutu sakamakon nutsewsr jirgin a ruwa amma dai babu wata sanarwa a hukumance.
A halin yanzu ana gudanar da aikin ceto domin gano yawan waɗanda hatsarin ya rutsa da su, tare da tantance girman asarar rayuka da dukiyar da aka yi, in ji DCL Hausa.
Mutum 9 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa
Wata majiya ta bayyana cewa jirgin ruwan ya gamu da hatsari ne a garin Zalla Bango, da ke yankin karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkato.
Wani mazaunin garin, Zayyanu Zalla Bango ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Legit Hausa, ya ce zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum tara.
Ya ce wannan shi ne karo na uku da aka samu irin wannan hatsarin cikin makonni biyu a yankin, inda ya roki gwamnati ta tashi tsaye don magance lamarin.
Jirgin ruwa na 3 ya yi hatsari a jihar Sakkwato

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Malamin da ya fi 'tsufa' yana wa'azi ya bar duniya yana shekaru 95
Zayyanu ya ce:
"Lamarin ya faru ne a garin Zalla Bango, karamar hukumar Sabon Birni kuma shi ne kifewar jirgin ruwa na uku a cikin makonni biyu, muna cikin halin tashin hankali da fargaba.
"Hatsarin farko da ya faru mutun 7 suka mutu, na biyu kuma an yi sa'a babu wanda ya mutu.
"Amma hatsarin jirgin ruwan jiya Alhamis kuma, an tabbatar da mutuwar mutum tara, duka sun gudo ne daga gidajensu domin tsera daga harin yan bindiga."

Source: Facebook
Sai dai mazauna yankin sun bayyana cewa hukumomi ba su kai dauki don ceto wadanda hatsarin ya rutsa da su a kan lokaci ba.
Wani mazaunin yankin na daban, Dahiru Habib ya tabbatar mana cewa hatsarin ya auku ne a tsakanin kauyen Mallamai da Zalla Bango, kuma ana fargabar mutum 10 suka mutu.
Jirgin ruwa dauke da mutum 90 ya nutse da Neja
A wani labarin, kun ji cewa an kara samun hatsarin jirgin ruwa da ya hallaka gomman mutane a yankin karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.
Hatsarin jirgin ruwan, wanda ya dauko mutane kusan 100, ya yi sanadiyyar mutuwar fasinjoji sama da 30.
Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya faru ne a kauyen Gausawa, da ke.yankin Malale, inda aka tabbatar cewa mutum 90 ne ke cikin jirgin lokacin da hatsarin ya auku.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

