Bayan Nasarar Dalibanta a NECO, Gwamnatin Kano za Ta Dauki Malamai 2, 600 Aiki

Bayan Nasarar Dalibanta a NECO, Gwamnatin Kano za Ta Dauki Malamai 2, 600 Aiki

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na shirin daukar ma’aikata 4,315 domin kara bunkasa koyar wa a jihar Kano
  • Amma a wannan karon, Gwamnan ya bayar da umarnin a dauki dalibai sama da 2,000 su fara koyar wa a makarantu daban daban a jihar
  • Matakin na zuwa a wani yanayi na kara karfafa wa harkar ilimi bayan daliban jihar sun doke sauran jihohin Najeriya a jarrabawar NECO ta bana

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta dauki dalibai malamai 4,315 domin kara karfafa ilimi.

Ya bayyana cewa wandanda za a dauka aikin, suna daga cikin wadanda ke koyar wa na wucin gadi a wasu makarantun da ke jihar.

Kara karanta wannan

Sakkwato: Shugabannin makarantun sakandare 6 sun tsunduma kansu a matsala

Gwamnatin Kano za ta dauki sababbin malamai
Hoton Gwamna Abba a cikin wasu daga cikin daliban Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a yayin wani taron kaddamar da sababbin malaman a birnin Kano a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba zai inganta ilimi a jihar Kano

The Guardian ta ruwaito cewa Gwamna Abba ya ce wannan matakin na daga cikin tsare-tsaren gwamnatinsa na farfado da martabar ilimi a jihar Kano.

A cewarsa, kowa ya sani cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban al'umma da kuma gina jiha da za ta samu bunkasar da ake bukata.

A kalaman Gwamnan:

"Wannan ba biki ne kawai ba, tabbaci ne na cewa mun yi imanin ilimi shi ne ginshikin ci gaban al'ummarmu."

Gwamna Abba ya kara wa malamai kaimi, inda ya yi kira gare su da su gudanar da aiki da gaskiya da himma domin gina tarbiyyar yara.

Kiran Gwamna Abba ga malaman Kano

Abba ya kuma jaddada cewa, gwamnati tana sa ran ganin cewa malamai za su zage dantse wajen koyarwa da nuna kishin kasa da sadaukarwa ga aikin da aka dora masu.

Kara karanta wannan

Daga Kaduna, Taraba da wasu jihohi ake kai hari a Filato inji rahoton gwamnati

Baya ga daukar sababbin malamai 4,315 da aka riga aka kaddamar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa gwamnati ta amince da daukar karin malamai 2,616 ta hukumar SUBEB.

Za a dauki malamai sama da 2000 a Kano
Hotunan Gwanmna Abba Kabir Yusuf da dalibai mata (H), da maza (D) a Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar na aiwatar da muhimman sauye-sauye a fannin ilimi, ciki har da gina sababbin makarantu da yi wa tsofaffin kwaskwarima.

Abba Kabir Yusuf ya kuma cewa za a rarraba kayan koyo da koyarwa a kananan hukumomi 44 na jihar, da kuma karin girma ga dubunnan malamai.

Gwamnan ya ce:

“Wannan sauyi da muke aiwatarwa bai taba faruwa a tarihin jihar Kano ba."

Kwankwaso ya yi alfahari da harkar ilimin Kano

A baya, kun samu labarin cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana jin dadinsa kan nasarar daliban Kano.

A sakon da ya fitar a ranar Alhamis, Sanata Kwankwaso ya ce nasarar da daliban su ka samu a wannan jarrabawa na nuna irin kokarin da ake yi wajen farfado da sha’anin ilimi a Kano.

Sanata Kwankwaso ya ce irin wannan sakamako yana nuna ci gaban da ake samu sakamakon gyare-gyaren da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi a fannin ilimi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng