Majalisar Rivers Ta ba Fubara Umarnin Gaggawa kan Kasafin Kudi da Kwamishinoni
- Majalisar dokokin Jihar Rivers ta dawo yin zama bayan karewar dokar ta-baci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kakaba
- 'Yan majalisar sun bukaci Gwamna Siminalayi Fubara ya aika musu da sunayen wadanda zai nada kwamishinoni domin tantancewa
- Haka kuma majalisar ta nemi a duba yadda kudin jihar suka tafi a lokacin mulkin shugaban riko da aka nada a lokacin dokar ta-baci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers – Majalisar dokokin jihar Rivers ta dawo gudanar da zama bayan dakatarwar da aka yi sakamakon dokar ta-baci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana a watan Maris.
Wannan shi ne zama na farko cikin wata shida da aka yi a jihar sakamakon rikici tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da wanda ya gabace shi, Nyesom Wike.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa zaman farko da aka yi a majalisar ya samu jagorancin shugabanta, Martins Amaewhule, inda aka tattauna muhimman batutuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun a ranar 18 ga Maris, shugaban kasa ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da kuma yan majalisar dokoki tare da kafa dokar ta-baci.
Amma daga bisani, a ranar 17 ga Satumba, Shugaba Tinubu ya kawo karshen wannan tsari tare da mayar da tsarin dimokuradiyya a jihar.
Umarnin 'yan majalisar Rivers ga Fubara
A yayin zaman, shugaban masu rinjaye a majalisar, Major Jack, ya gabatar da kudiri inda ya bukaci Gwamna Fubara ya gaggauta aika jerin sunayen wadanda zai nada a kwamishinoni.
Ya bayyana cewa, hakan na da muhimmanci domin kafa cikakkiyar majalisar zartarwa ta jihar wacce za ta taimaka wajen tafiyar da al’amuran mulki cikin koshin lafiya.
Punch ta wallafa cewa Jack ya ce wannan bukatar ta yi daidai da kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyar zaman lafiya da ta dawo da dimokuradiyya a jihar.

Kara karanta wannan
Ibas: Mutumin Tinubu ya fara fuskantar matsala bayan cire dokar ta baci a jihar Ribas
Majalisar Rivers za ta binciki Ibas
Majalisar ta kuma nemi a yi cikakken nazari kan yadda kudin jihar suka tafi a lokacin Ibok-Ete Ibas da aka nada a matsayin shugaban rikon kwarya yayin dokar ta-baci.
Yan majalisar sun nuna cewa akwai bukatar a bincika kwangilolin da aka bayar da kuma yadda aka kashe kudi daga asusun jihar, domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Jack ya yi nuni da cewa duk da an yi da zabukan kananan hukumomi a Agusta da suka samar da shugabanni 23, akwai sauran abubuwa da dama da suka bukaci bayyana ga jama’ar jihar.

Source: Twitter
Umarni na 2 da majalisa ta ba Fubara
'Yan majalisar sun kuma bukaci gwamnati ta turo kasafin kudi na ragowar shekarar domin samun sahalewar majalisar.
Sun jaddada cewa za su ci gaba da aiki tare da Gwamna Fubara wajen samar da sabuwar manufar da za ta dace da muradun jama’ar jihar.
Magoya bayan Fubara sun taru a Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa dandazon magoya bayan gwamna Siminalayi Fubara sun taru a kofar gidan gwamnati domin masa maraba.
Rahotanni sun nuna cewa mutanen sun taru ne da tsammanin cewa gwamna Fubara zai koma ofis bayan dokar ta-baci.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa mutanen sun gaji da zama, sun watse saboda rashin bayyanar Fubara bayan dogon jira da suka yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

