Nasara daga Allah: An Kama Tireloli 2, Wasu Motoci Cike da Kayan 'Yan Ta'adda

Nasara daga Allah: An Kama Tireloli 2, Wasu Motoci Cike da Kayan 'Yan Ta'adda

  • Rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas ta cafke tirela ɗauke da manyan kayayyakin da ake shirin kai wa ‘yan ta’adda
  • Rahotanni sun nuna cewa an gano buhunan taki 700, magunguna da sauran kayayyakin da ake ɓoye a cikin motar
  • Sojojin sun kuma tare wasu motoci kirar Sharon guda biyu da wata mota da kayan dinki da ake zargi na ‘yan ta’adda ne

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe – Rundunar haɗin gwiwa ta tsaro a Arewa maso Gabas ta samu nasarar cafke wata tirela mai ɗauke da kayan da ake shirin kai wa ‘yan ta’adda a yankin.

Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 16 ga Satumba yayin wani shirin yaki da ta’addanci mai taken Operation Desert Sanity IV.

Kara karanta wannan

Sauki ya samu da aka hallaka tantirin dan bindiga yana cikin shirya kai mummunan hari

Motocin da sojoji suka kama da ake zargin za a kai wa 'yan ta'adda kaya
Motocin da sojoji suka kama da ake zargin za a kai wa 'yan ta'adda kaya. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa bayanin rundunar ya nuna cewa an samu nasarar ne sakamakon sahihan bayanan sirri da aka tattara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa an cafke motar ne a kan titin Nguru–Gashua da ke jihar Yobe da misalin ƙarfe 7:40 na safe.

Kayan da sojoji suka gano a tirelar

Rundunar ta bayyana cewa a cikin tirelar an samu buhunan taki 700, katin magunguna 27 da wasu kayyaki.

Sojojin sun kara da cewa an ɓoye abubuwan ne ƙarƙashin wasu kayayyaki don kauce wa binciken jami’an tsaro.

Binciken ya nuna cewa an shirya jigilar kayayyakin zuwa Jamhuriyar Nijar, abin da ke nuna cewa akwai hanyar sadarwa ta ƙetare iyaka da ke tallafawa ‘yan ta’adda.

Sojoji sun kara kama wasu motoci

A rana guda, da misalin ƙarfe 10:30 na safe, sojojin da ke kan hanyar sun kuma tare wasu motocin Sharon guda biyu da wata tirela ɗauke da kaya da na'urar sola.

Kara karanta wannan

Trump ya ga ta kansa, an masa ihu ana zanga zanga a London

Rahotannin sirri sun nuna cewa an tanadi wasu daga cikin kayayyakin ne don dinka kayan sawa ga ‘yan ta’adda da kuma samar musu da wutar sola a sansanoninsu.

Dukkan direbobin, mataimakansu da kayan da aka kwace na hannun jami’an tsaro, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike da kuma kokarin kamo wadanda ke da hannu a jigilar kayan.

Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Martanin rundunar sojin Najeriya

Kwamandan Rundunar ya tabbatar da cewa sojojin na ci gaba da kasancewa cikin shiri domin katse duk wata hanyar tallafi da ‘yan ta’adda ke dogaro da ita a Arewa maso Gabas.

Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanai a kan lokaci don taimakawa wajen nasarar ayyukan tsaro.

Babban kwamandan sojojin ƙasa ya yaba wa dakarun da suka gudanar da aikin, yana mai cewa irin wannan nasara na taimakawa wajen rage ƙarfin ‘yan ta’adda.

An kama mai kera bindiga a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kama wani mutum da ake zargi yana hada bindigogi a jihar Filato.

Rahotanni sun nuna cewa an kama mutumin ne yayin wani samame da dakarun Najeriya suka yi a karamar hukumar Barikin Ladi.

Kara karanta wannan

Karfin hali: 'Yan bindiga sun gabatar da manyan bukatu 3 kan sulhu a Katsina

Yayin da sojoji suka yi bincike a gidan mutumin, an samu bindigogi kirar gida har guda 12 yayin da aka samu bindiga kirar pistol daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng