Abin Kunya: Yan Sanda Sun Kama Malamin Addinin Musulunci Dauke da 'Kayan Laifi'
- Yan sanda sun cafke wani malamin addinin musulunci dauke da wani abu da ake zargin naman jikin dan adam ne a jihar Oyo
- Kakakin rundunar yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso ya ce malamin ya shaida masu cewa a jihar Legas ya saya naman
- Bugu da kari, yan sandan Oyo sun kwato wata mota a wurin binciken ababen hawa bayan direba ya fita ya gudu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta kama wani malamin addinin Musulunci da aka bayyana sunansa a matsayin Alfa Bashiru.
Jami'an yan sanda sun kama malamin ne bisa zarginsa da mallakar wasu sassan jikin ɗan adam.

Source: Twitter
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Adewale Osifeso, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani saƙo da aka wallafa a shafin X na rundunar.

Kara karanta wannan
Yan sanda sun wanke malamin addini da aka ce yana yawo da bindiga, sun yi karin haske
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kama malami da naman dan adam
Ya ce dakarun yan sandan da ke sintiri a kan babban titin tarayya a Oyo ne suka tare farar mota da wanda ake zargin ke ciki mai lambar rijista XA 551 IRG.
Kakakin yan sandan ya ce an kama malamin ne a yankin Toll Gate na babban titin Ibadan da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Laraba.
Osifeso ya ce, lokacin da yan sanda suka titsiye wanda ake zargin da tambayoyi, ya bayyana cewa ya saya naman ne a jihar Legas.
Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce yanzu haka an tura malamin musuluncin zuwa sashen binciken manyan laifuka na Oyo (SCID) da ke Iyaganku, domin ci gaba da bincike.
"An kai naman da ake zargin na dan adam ne wurin bincike domin tabbatar wa da kuma gano asalinsa,” in ji Osifeso.
Yan sanda sun kama mota a Oyo

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun farmaki bayin Allah suna ibada, an rasa rayukan mutane 22 a Nijar
A wani lamari daban kuma, rundunar yan sandan Oyo ta bayyana cewa jami’anta sun dauko wata mota Toyota Camry mai lambar rajista 957 JX da aka tsere aka bar ta.
Osifeso ya ce ’yan sanda sun umarci motar da ta tsaya a wurin da suke binciken ababen hawa, amma direban ya fita ya tsere ya bar motar, in ji rahoton Vanguard.
Ya kara da cewa sun dauke motar zuwa hedikwatar rundunar, inda ya bukaci duk wanda ke da hujja ta mallakar motar ya zo da takardun shaida ko kuma ya tuntubi rundunar ’yan sanda.

Source: Facebook
Kakakin yan sandan ya ce aikin bincike a kan titi ba wasa ba ne, sai dai wani matakin tsaro na zahiri don tabbatar da zaman lafiya da kuma kare rayukan jama’a da matafiya a jihar Oyo.
Ya kara da cewa kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Femi Haruna, ya gode wa jama’a bisa goyon bayansu da fahimta, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kokarin yaki da laifuka domin samar da tsaro.
Yan sanda sun kama sojan bogi a Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa ‘yan sandan Ondo sun kama Abdullahi Saliu wanda ya yake sojan gona da Kanal a rundunar soji yana damfarar mutane kudi.
Mutumin ya rika amfani da sunan babban jami’in soji, inda ya damfari mutane sama da ₦1.3m ta hanyar yin alkawarin samar musu da aikin gwamnati.
Masu bincike sun gano cewa Abdullahi Saliu, wani dan damfara ne da ya dade yana gudanar da ayyukansa na damfara a jihohi daban-daban.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
