Wike Ya Aika Sako ga Shugaba Tinubu kan Janye Dokar Ta Baci a Rivers

Wike Ya Aika Sako ga Shugaba Tinubu kan Janye Dokar Ta Baci a Rivers

  • Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi martani kan janye dokar ta-baci a jihar Rivers mai arzikin mai
  • Nyesom Wike ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan dawo da mulkin dimokuradiyya a jihar
  • Ministan ya bayyana cewa tun da farko, Shugaba Tinubu ua ceci jihar Rivers ta hanyar ayyana dokar ta baci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na janye dokar ta-baci a jihar Rivers.

Nyesom Wike ya yabawa Shugaba Tinubu bisa mayar da tsarin mulkin dimokuraɗiyya a jihar Rivers.

Wike ya yabawa Shugaba Tinubu
Hoton Shugaba Bola Tinubu da Nyesom Wike Hoto: @GovWike, @DOlusegun
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakin ministan, Lere Olayinka, ya sanya a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya yabawa Shugaba Tinubu

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi dalilin janye dokar ta baci a Rivers

Ministan ya ce shugaban kasa ya sake nuna cikakkiyar jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da dorewar dimokuraɗiyya a kasar nan.

Ya bayyana cewa matakin da ya dauka cikin gaggawa ta hanyar ayyana dokar ta-baci, ya ceci jihar Rivers.

Wike ya bayyana cewa matakin da shugaban kasan ya dauka, ya kara dawo da kwarin gwiwar mutanen Rivers kan jagorancinsa.

Ministan ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a jihar da su yi aiki tare cikin haɗin kai don amfanin jama’ar jihar da ci gaban ta gaba ɗaya.

"Ministan babban birnin tarayya Abuja ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan dawo da mulkin dimokuradiyya a jihar Rivers, ta hanyar janye dokar ta-bacin da aka kakaba."
"Ya kuma yabawa mutanen Rivers bisa amincewa da shugabancin Tinubu da kuma goyon bayan da suke ci gaba da bayarwa ga kokarinsa wajen dawo da Najeriya kan tafarkin bunkasa da cigaba."

- Lere Olayinka

Wike ya yi gargadi kan Rivers

Ministan ya kuma yi gargadi ga masu neman tayar da hankali, musamman waɗanda ke son amfana da rikici, da su nesanta kansu daga jihar.

Kara karanta wannan

Dogara ya bankado abubuwan da ya ce Buhari ya lalata kafin ba Tinubu mulki

“Daga yanzu zuwa gaba, labaran da za su fito daga Jihar Rivers ba za su wuce na zaman lafiya, cigaba da ci gaban al’umma ba."

- Lere Olayinka

Wike ya yabi Shugaba Bola Tinubu
Hoton ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Karanta wasu labaran kan Wike

Tinubu ya kawo dalilin janye dokar ta-baci

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kawo dalilin da ya sanya ya janye dokar ta-baci a jihar Rivers.

Shugaban kasan ya bayyana cewa ya janye dokar ta-bacin ne bayan alamu sun nuna masa cewa masu ruwa da tsaki a jihar, sun shirya rungumar zaman lafiya.

Ya bayyana cewa tun da farko ya sanya dokar ta bacin ne bayan harkokin mulki sun tsaya a jihar, sakamakon sabanin da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da 'yan majalisar dokoki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng