NECO: Matakan Gwamna Abba Sun Fara Aiki, Kano Ta Shiga Gaban Jihohin Najeriya
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna farin cikinsa bisa yadda daliban Kano suka ci jarabawar kammala sakandire ta NECO a bana 2025
- A sakamakon jarabawar da hukumar NECO ta fitar yau Laraba, jihar Kano ta shiga gaban a jerin jihohin da suka samun sakamako mai kyau
- Gwamnatin Kano ta ce wannan nasara alama ce da ke nuna cewa matakan da Gwamna Abba ke dauka suna kan hanya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta dare mataki na farko a jerin jihohin da suka fi cin jarabawar kammala makarantun sakandire watau NECO.
Kano ta shiga gaban duka jihohin Najeriya a sakamakon jarabawar da hukumar shirya jarabawar sakandire ta kasa (NECO) ta fitar yau Laraba.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa ya tabbatar da hakan a wata sanarwada ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan babban nasara ta samo asali ne daga sauye-sauye da zuba jari mai tsoka da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a fannin ilimi tun farkon hawansa kan mulki.
Kano ta shiga gaba a cin jarabawar NECO
A yayin da yake bayyana sakamakon a Minna, Jihar Neja, Shugaban NECO, Farfesa Ibrahim Wushishi, ya ce kashi 60.26 na wadanda suka zauna jarabawar sun ci.
Ya ce daga cikin ɗalibai 1,358,339 da suka zauna jarrabawar NECO a watan Yuni/Juli, ɗalibai 818,492 (60.26%) sun samu sakamako mai kyau na aƙalla darussa biyar har da Lissafi da Turanci.
Bugu da ƙari, ɗalibai 1,144,496 (84.26%) sun samu darussa biyar ko fiye, ba tare da darussan Lissafi da Turanci ba.
Jihar Kano ce ta yi fice da ɗalibai 68,159 (5.020% na jimilla) da suka samu darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.
Lagos ta biyo baya da ɗalibai 67,007 (kashi 4.930%), yayin da Oyo ta zo ta uku da ɗalibai 48,742.
Gwamna Abba ya yi farin ciki da nasarar
Da yake martani ta hannun mai magana da yawunsa, Gwamna Abba ya bayyana wannan nasarar a matsayin wata alama da ke nuna yadda gwamnatinsa ta ba ilimi fifiko.
Ya kuma bayyana farin cikinsa, yana mai jaddada aniyarsa ta kara zage damtse wajen gyare-gyare a harkar ilimi tare da yabawa dukkan masu ruwa da tsaki a fannin.

Source: Facebook
Abba ya ce:
“Tsare-tsarenmu sun fara haifar da sakamako mai kyau. Wannan bajintar da ɗaliban Kano suka yi hujja ce cewa muna tafiya a hanya madaidaiciya.
"Ilimi ya kasance muhimmin ginshiƙinmu, kuma ba za mu gajiya ba wajen tabbatar da cewa babu wani haifaffen Kano da aka bari baya a harkar karatu.”
Gwamnan Kano ya biyawa dalibai NECO
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Kano ta dauki nauyin biyan kudin jarrabawar NECO da NBAIS na dalibai 3,526 daga makarantu daban-daban a jihar.
Daliban za su yi jarrabawar kammala Sakandare ta NECO da ta Hukumar Nazarin Harshe da Ilimin Addinin Musulunci (NBAIS) a kyauta a jihar Kano.
Gwamna Abba ya amince da yiwa daliban rajistar jarrabawar ne bayan sun ci jarrabawar cancantar a biya masu kudin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


