Yadda Direbobin Dangote ke Samun Alheri Sama da Masu Digiri a Najeriya
- Alhaji Aliko Dangote ya tanka wa kungiyar direbobin motocin dakon mai da gas (NUPENG), wacce ta zarge shi da yunkurin kashe masu aiki
- Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Group ya ce direbobinsa na samun kudin da ya fi albashin masu aiki da kwalin digiri a Najeriya
- Attajirin dan kasuwar ya ce sababbin motocin daya saya da nufin raba fetur kyauta za su samar da dubanninn ayyuka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa direbobin kamfaninsa na samun albashi mai tsoka.
Attajirin dan kasuwar, wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka ya ce direbobin da ke aiki a karkashin kamfaninsa na samun albashin da ya fi na mafi yawan masu digiri a ƙasar.

Source: Getty Images
Dangote ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi kwanan nan wacce ta fara yaduwa ranar Talata, 16 ga watan Satumba, 2025, kamar yadda Premium Times ta kawo.

Kara karanta wannan
Dangote ya ce ana neman ya saka tallafin man fetur na Naira tiriliyan 1.5 a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda NUPENG ta taso Dangote
Ana ganin dai Dangote ya bayyana haka ne a a matsayin martani ga zargin da ƙungiyar direbobin man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG) ta yi.
NUPENG ta zargi Dangote da abokinsa na kasuwanci, Sayyu Aliu Dantata, da yunkurin mamaye gaba daya kasuwanci a sashen rarraba man fetur da iskar gas na ƙasa tare da tauye ’yancin ma’aikata.
Ta kuma yi zargin cewa Dangote ya tilasta wa sababbin direbobi da aka ɗauka su rattaba hannu cewa ba za su shiga kowace ƙungiyar direbobin mai da gas ba, in ji rahoton Channels tv.
NUPENG ta yi barazanar fara yajin aiki na ƙasa baki ɗaya daga ranar Litinin 8 ga Satumba, domin nuna adawa da abin da ta kira "mugayen manufofin aiki" na Matatar Dangote.
Dangote ya mayar sa martani
A cikin hirar, Dangote ya bayyana cewa motoci masu amfani da gas watau CND da kamfaninsa ya a kaddamar ba su hana kowake direban motocin kasuwa aikinsa ba.
Attajirin ya ce:
“Motocin da muka ƙaddamar ba su hana kowa aikin da yake yi ba. An ce za a rasa ayyuka, shin injinan roba ne za su tukasu? Kowace mota muna mutum shida.
"Don haka motocin da ake husuma a kansu za su samar da ayyuka 24,000. Bayan shekaru biyar ba tare da haɗarin mota ba, direba zai iya neman rancen gida.”

Source: Getty Images
Nawa direbobin motocin Dangote ke samu?
Dangote ya ƙara da cewa albashin direbobin nasa ya ninka mafi ƙarancin albashi na ƙasa sau uku zuwa hudu, inda wasu daga cikinsu ke samun abin da ya zarce albashin yawancin masu digiri.
“Direbobinmu na samun albashi fiye da masu digiri. Idan aka duba abin da suke samu a wata, ya fi nunka mafi ƙarancin albashin ƙasa sau hudu," in ji shi.
Wani direban babbar mota, Faisal Yusuf ya ce duk da bai san tsarin aikin Dangote ba amma maganarsa ta samun nunkin mafi karancin albashi gaskiya ne.
Da yake tattaunawa da wakilin Legit Hausa kan kalaman Dangote, Faisal ya ce idan aiki na zuwa a kai-a-kai, mutum zai iya samun N200,000 zuwa N500,000 a wata.
"Maganar Dangote tana kan hanya, babu doreban da zai ajiye maka mota ya dauki albashin N100,000 ko N150,000. Aikin tuki yana da wahala amma ana samun kudi," in ji shi.
Man feturin Dangote ya fi araha a Togo?
A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta karyata ikirarin da kungiyoyin mai irinsu DAPPMAN da NUPENG ke yi na cewa feturinta ya fi arha a Togo.
A wata sanarwa da matatar ta fitar, ta bayyana cewa irin wannan zargi da kungiyoyin ke yi da mara tushe ballantana makama.
Matatar ta kuma yi watsi da bayanin da DAPPMAN ta fitar a jaridu a ƙarshen mako, inda ta ce an shirya bayanan ne domin karkatar da hankalin jama'a daga gaskiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
