Yan Sanda Sun Wanke Malamin Addini da Aka Ce Yana Yawo da Bindiga, Sun Yi Karin Haske

Yan Sanda Sun Wanke Malamin Addini da Aka Ce Yana Yawo da Bindiga, Sun Yi Karin Haske

  • Rundunar ’yan sanda a Najeriya ta kammala bincike bayan zargin wani malamin addinin Kirista na yawo da bindiga
  • Rundunar da ke Lagos ta ce ta wanke babban Faston House on the Rock, Fasto Paul Adefarasin, bayan bidiyonsa da bindiga ya bazu
  • 'Yan sanda sun tabbatar da cewa abin da aka gani a bidiyon ba bindiga ba ce, illa kayan kare kai mara lahani

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Rundunar ’yan sandan Jihar Lagos ta fitar da bayanan karshe game da binciken malamin addinin Kirista.

Rundunar ta bayyana cewa ta wanke babban Faston House on the Rock, Paul Adefarasin, daga duk wani laifi bayan wani bidiyo ya nuna shi yana riƙe da abin da ake zargin bindiga.

Yan sanda sun wanke Fasto a Lagos
Fasto Paul da kakakin yan sanda a Lagos. Hoto: CPS Benjamin Hundeyin.
Source: Facebook

Yan sanda sun magantu game da zargin Fasto

Kara karanta wannan

Dan majalisar Filato da ake nema ruwa a jallo ya mika kansa, ICPC ta tsare shi

A sanarwar da kakakin rundunar, Abimbola Adebisi ya fitar wanda Punch ta samu, an tabbatar da cewa Adefarasin ya kai kansa hedkwatar ’yan sanda a Ikeja domin amsa tambayoyi.

Binciken ’yan sanda ya nuna cewa abin da aka gani a cikin bidiyon da ya bazu bindigar wasa ne, ba bindiga ko makami mai kisa ba.

Sanarwar ta ce:

“Bayan cikakken bincike, wanda ya haɗa da tambayoyi da kuma rubuta bayanin gargadi daga Fasto Adefarasin, an tabbatar da cewa abin da ake magana a kai bindigar wasa ne, ba makami mai kashewa ko bindiga ba.
“Dangane da sakamakon bincikenmu, Rundunar ’yan sandan Jihar Lagos ta yanke shawarar cewa babu isasshen dalilin ci gaba da shari’ar. An dakatar da shari’ar nan take."
Yan sanda sun kammala binciken Fasto kan mallakar bindiga
Babban Sufetan yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Dokar da ta yi magana kan bindiga

Rundunar ta ƙara da cewa tana jajirce wajen gudanar da ayyukanta da gaskiya tare da bin doka domin tabbatar da tsaron jama’a da adalci.

Wannan na zuwa ne bayan rahoton watan Yuni, lokacin da Kwamishinan ’yan sanda Olohundare Jimoh ya bayyana cewa nuni da bindigar wasa ga mutum na iya zama laifi.

Kara karanta wannan

Malami ya shiga rikici da gwamna, ana zarginsa da ingiza ta'addanci a jihar Kebbi

A wancan lokacin, Jimoh ya bayyana a Channels TV cewa bindigar wasa na cikin kayan da aka haramta a Najeriya, kuma amfani da shi don tsoratarwa na iya zama laifi.

Ya ƙara da cewa malamin addinin da mutumin da aka zarga da yi masa barazana a bidiyon za a yi musu tambayoyi, The Guardian ta ruwaito.

Bidiyon da ya bazu a Yuni ya nuna Faston yana zaune a cikin mota kirar Range Rover yana riƙe da na’urar yayin tattaunawa da wani mutum.

Adefarasin ya musanta cewa ya taɓa riƙe bindiga, inda ya jaddada cewa abin da yake riƙe da shi ba makami mai lahani ba ne.

Yan sanda sun kama yan fashi 35

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Lagos ta kama mutane 35 da ake zargi da fashi da makami a titi a yankunan Ajah da Elemoro.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama su ne a yayin atisayen sintiri da jami'an tsaro suka kaddamar don dakile ayyukan masu laifi.

Kakakin 'yan sandan jihar ya ce ana ci gaba da kai irin wadannan farmaki a jihar don tabbatar da doka da oda da maganin bata gari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.