Yunwa Ma da Ranarta: Kashim Shettima Ya Fadi Babban Abin da Ke Hada kan Al’umma

Yunwa Ma da Ranarta: Kashim Shettima Ya Fadi Babban Abin da Ke Hada kan Al’umma

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bukaci ƙasashe su haɗa kai wajen yakar yunwa, ƙirƙirar arziki da bunƙasa noma
  • Shettima ya ce Najeriya tana da matasa da filaye masu faɗi, ya kuma jaddada bukatar jari da ban ruwa da kayayyakin noma
  • Ministan noma, Abubakar Kyari, ya bayyana shirin saka hannun jari na dala biliyan 3.14 domin bunkasa masarufi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya bukaci ƙarin haɗin gwiwa na ƙasa da na yanki domin kawar da yunwa.

Kashim Shettima ya ce samar da arziki da bunƙasa damarmakin noma a Afirka shi ne babban abin da zai kawo ci gaba.

Kashin Shettima ya magantu kan hanyar yaki da talauci
Mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Twitter

Shettima ya fadi abin da ke hada kan al'umma

Mataimakin shugaban kasa ya bayyana haka ne ne yayin jawabi a taron FAO Hand-in-Hand a Abuja, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Ribas: Peter Obi ya zargi gwamnatin Najeriya da yi wa dimokuradiyya kisan mummuke

Shettima ya ce yunwa barazana ce ta tsaro wacce ke bukatar haɗin kan duniya baki ɗaya.

Ya ce:

“Babu abin da ke haɗa bil’adama kamar yunwa, Ita ce babbar mai daidaitawa wacce ke bayyana rauninmu da haɗarin rayuwarmu gaba ɗaya."

Kashim Shettima ya bayyana matasa da filayen noma na Najeriya a matsayin manyan jarin ƙasa, ya ce shirin ci gaban ƙasa zai fitar da miliyoyi daga talauci.

Ya ce shirin zai samar da ayyukan yi miliyan 21, ya kawo wadatar abinci ta hanyar saka hannun jari a sassa daban-daban na noma.

Damarmaki da Najeriya ke da shi

Shettima ya bayyana ginshiƙan tsarin Najeriya uku: daidaita jari da bukatun ƙasa, samar da yanayi mai kyau da kuma shirya ayyukan noma masu samun riba.

Ya ce Najeriya tana da damar ban ruwa mai girman hekta miliyan uku, amma ana amfani da kasa da kashi 10 cikin ɗari kawai.

“Shekarar saka jari a ban ruwa na iya ninka amfanin gona sau uku, ta fitar da mu daga dogaro da damina."

Kara karanta wannan

Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya

- Kashim Shettima

Kashim Shettima ya bukaci hadin kai domin yaki da talauci
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Facebook

Kashim Shettima ya kuma jaddada damar da ke cikin yarjejeniyar kasuwanci ta AfCFTA, inda ya ce Najeriya na iya zama cibiyar noma da fitar da kayan gona.Kashim Shettima ya kuma jaddada damar da ke cikin yarjejeniyar kasuwanci ta AfCFTA, inda ya ce Najeriya na iya zama cibiyar noma da fitar da kayan gona.

Ya kara da cewa:

“Tare da mutane miliyan 230 da tattalin arzikin dijital mafi girma a Afirka, Najeriya tana bude ƙofa ga kasuwanci."

Ministan noma ya yi albashir ga al'umma

Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari, ya gabatar da shirin saka hannun jari na dala biliyan 3.14 karkashin FAO, Punch ta ruwaito.

Shirin ya haɗa da tumatir, rogo, masara, madara da kifaye, ya ce zai fitar da miliyoyi daga talauci tare da samar da ayyukan yi.

Kyari ya ce shirin ya samu dala biliyan 1.75 daga gwamnati da biliyan 1.39 daga masu zaman kansu domin tallafa wa aikin noma a ƙasa.

Kara karanta wannan

Karfin hali: 'Yan bindiga sun gabatar da manyan bukatu 3 kan sulhu a Katsina

Legit Hausa ta tattauna da dan PDP

Matashi Aliyu Ahmad a Gombe ya ce wannan duk rashin hujjoji ne na kare kansu saboda bakar yunwa da suka jefa mutane.

Ya ce:

"Abin kunya ne bayan jefa al'umma a halin kunci kum a zo ana maganar wai ynuwa tana kan mutane."

Matashin dan PDP ya ce babu abin da yunwa ke haddasa wa illa rashin tsaro kamar yadda talauci ke yi.

Shettima ya yi albishir ga manoman Najeriya

Kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya umarci PFSCU ta hanzarta rabon lamunin Naira biliyan 250 ga kananan manoma.

Ya bukaci samar da ingantaccen hanyar aiwatar da shirin don tabbatar da cewa kuɗin ya isa ga manoma a Najeriya cikin lokaci.

Gwamnonin jihohi da dama sun yaba da shirin tare da roƙon a ƙara tallafi ga manoma domin tabbatar da wadatar abinci a kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.