NECO Ta Fadi Lokacin Sakin Sakamakon Jarrabawar Dalibai na Shekarar 2025
- Hukumar NECO ta tabbatar da cewa za ta saki sakamakon jarrabawar SSCE ta 2025 a ranar Laraba, 17 ga Satumba a jihar Neja
- Shugaban hukumar, Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi, ne zai jagoranci fitar da sakamakon a shelkwatar NECO da ke Minna
- Haka kuma, hukumar za ta gudanar da bikin karrama ma’aikatanta da suka yi ritaya da domin jinjina masu a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar shirya jarrabawar NECO ta sanar da shirin sakin sakamakon jarrabawar SSCE) na shekarar 2025
Ta sanar da cewa za a saki sakamakon a ranar Laraba 17 ga Satumba, 2025 domin ba dalibai damar ganin abin da su ka samu.

Source: Facebook
A labarin da ya kebanta ga Nigerian Tribune, ta ruwaito cewa Shugaban hukumar NECO, Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi, ne zai gabatar da sakamakon a hukumance.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana jiran jawabin Shugaban NECO
A yayin wani taro na musamman da za a gudanar a shelkwatar hukumar da ke Minna, babban birnin Jihar Neja, ana sa ran Shugaban Hukumar zai yi jawabi.
Rahotanni sun bayyana cewa ma’aikatan hukumar za su halarci taron cikin yawa, da ake sa ran zai zama na tarihi ga jami'an NECO.
Ana sa ran dalibai da iyaye za su shiga shafin hukumar NECO domin duba sakamakon jarrabawar da aka dade ana jira.

Source: Original
Haka kuma ana sa ran hukumar NECO za ta gudanar da bikin karrama ma’aikata da suka yi ritaya da kuma na nuna ƙwazon aiki a ranar Alhamis.
Za a gudanar da taron a ranar 18 ga Satumba, 2025, da ƙarfe 10.00 na safe, a shelkwatar hukumar da ke Minna kwana daya bayan sakin sakamakon NECO.
Shugaban NASU ya yabi ma'aikatan NECO
Shugaban NASU na NECO, Kwamared Terndu Iorshagher, ya bayyana cewa tsofaffin ma'aikatan sun bayar da gagarumar gudunmawa, ba kawai ga NASU ba, har da hukumar gaba ɗaya.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji
A wannan biki, za a karrama ma’aikatan da suka yi ritaya daga aiki, tare da kaddamar da kyaututtuka daga kungiyar ma’aikata ta NASU, domin girmama su.
Ya ce:
“Ritaya ba ƙarshen rayuwa ba ce, sai dai sabon mataki ne na rayuwa. Muna fatan al’umma za ta ci gaba da amfana da su, kuma Allah ya ba su nasara a abin da za su sanya a gaba."
NECO ta saki sakamako
A baya, mun kawo labarin cewa Hukumar kula da jarrabawa ta ƙasa, wato NECO, ta saki sakamakon jarrabawar SSCE)na shekarar 2024 a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, a shekarar 2024.
Magatakardar NECO, Farfesa Dantani Wushishi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an fitar da sakamakon bayan an kammala tantance jarrabawar.
Farfesa Wushishi ya bayyana cewa an dakatar da wata makaranta a jihar Ekiti bisa zargin satar amsoshin jarrabawa kuma an sa ido a kan wasu wuraren zana jarabawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
