'Na Sha Fama,' Dangote Ya Fadi yadda aka Hana Shi Kafa Kamfani a Benue

'Na Sha Fama,' Dangote Ya Fadi yadda aka Hana Shi Kafa Kamfani a Benue

  • Aliko Dangote ya ce tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya nemi ya kawo ƙarshen shigo da siminti Najeriya
  • Ya bayyana yadda ya fuskanci cikas daga al’ummar jihar Benue a 2000 kafin ya kafa masana’anta Obajana
  • Attajirin ya bayyana cewa cin hanci da rashin gaskiya na hana ci gaban harkar mai da tattalin arzikin ƙasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Alhaji Aliko Dangote ya sake bude tarihi da kuma bayani kan kalubalen da ya sha a rayuwar kasuwancinsa da kuma yadda harkokin tattalin arziki ke tafiya a Najeriya.

A cewar sa, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya gayyace shi fadar shugaban ƙasa a 2000 don neman mafita ga matsalar shigo da siminti.

Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote
Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

A wani bidiyo da Imrana Muhammad ya wallafa a X, ya ce Obasanjo ya bukace shi ya nemo hanyar kawo ƙarshen shigo da siminti Najeriya.

Kara karanta wannan

Sulhu: 'Dan bindiga, Ado Aliero ya nemi afuwar mutanen da aka kashe wa 'yan uwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya bayyana wannan ne a wani jawabi inda ya kuma yi karin haske kan cikas da ke hana Najeriya cimma burin dogaro da kai a fannin mai da karafa.

An hana Dangote kafa kamfani a Benue

Dangote ya ce lokacin da Obasanjo ya umarce shi da ya kafa masana’antar siminti a shekarar 2000, ya fara niyya kafa kamfani a jihar Benue.

Sai dai al’ummar yankin sun ki amincewa da shirin, har ma suka ce ba za a taba ganin hakan ba sai bayan ransu.

Wannan ya tilasta shi ya sauya matsugunni zuwa Obajana a jihar Kogi, inda ya kafa babbar masana’antar siminti da ta zama ginshikin samar da kayan gini a Najeriya.

kalubalen harkar mai a Najeriya

Dangote ya bayyana cewa an dade ana fama da cin hanci da rashin gaskiya a harkar shigo da mai daga ƙasashen waje.

Ya ce yawanci ba a sauke kayan da jiragen da ke shigo da man fetur ke dauke da su saboda jami’an da ke duba kaya suna karɓar rashawa.

Kara karanta wannan

Najeriya ta rasa babban malamin Musulunci, shugaban limaman Ondo ya rasu

Ya koka da cewa cin hanci da rashawa da suka yi katutu a harkar ne suke jawo rashin sauke kayan baki daya.

Wani sashe na matatar Dangote a Legas
Wani sashe na matatar Dangote da ke Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Dangote ya yi karin haske kan shirin sa na raba fetur kyauta ga gidajen mai a Najeriya daga matatar man sa, wanda ya ce ya gamu da ƙalubale iri-iri daga masu ruwa da tsaki a fannin.

Maganar Dangote kan Ajakuta

Dangote ya yi tsokaci mai zafi kan batun kamfanin Ajakuta, inda ya bayyana cewa kamfanin karafan ya tsufa kuma ba za a iya farfaɗo da shi ba.

Rahoton Nairametrics ya nuna cewa Dangote ya kwatanta hakan da yunƙurin tasar da mamaci daga makabarta ko maras lafiya da ya kusa mutuwa don ya yi gudun mita 100.

Ya jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta samu ci gaba ba tare da masana’antar karafa ba, amma ya zama dole a rungumi sababbin fasahohi maimakon riƙe tsofaffi.

Dangote ya fara raba mai kyauta

A wani rahoton, kun ji cewa matar Dangote ta fara raba man fetur kyauta a Najeriya a ranar Litinin da ta wuce.

Kara karanta wannan

An nuna fuskar Kachalla Babaro da ya kai hari masallaci, ya kashe Musulmai

Hakan na zuwa ne bayan shafe kwanaki 'yan kasuwa da masu dakon mai suna bugawa da Dangote kan lamarin.

Sai dai duk da haka, Dangote ya ce ba gudu ba ja da baya, inda ya fara raba fetur a jihohi 10 da birnin tarayya Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng