Karfin Hali: 'Yan Bindiga Sun Gabatar da Manyan Bukatu 3 kan Sulhu a Katsina

Karfin Hali: 'Yan Bindiga Sun Gabatar da Manyan Bukatu 3 kan Sulhu a Katsina

  • 'Yan bindiga a Katsina sun gabatar da buƙatu uku manya ga gwamnati yayin da ake cigaba da magana kan sulhu
  • Kwamishinan tsaro ya ce rashin adalci da rushewar sulhu ne suka taimaka wajen ta’azzarar matsalar tsaro a jihar
  • Masana tsaro na ganin akwai buƙatar tantance waɗanda za a tallafawa a jihar musu don kauce wa ƙarfafa masu laifi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Matsalar 'yan bindiga a Arewacin Najeriya, musamman a jihar Katsina, na ci gaba da jefa al’umma cikin tashin hankali da asarar rayuka.

Duk da cewa a baya gwamnatin Katsina ta dage kan cewa ba za ta taɓa tattaunawa da 'yan fashin ba, sabon salo ya fara bayyana inda al’umma ke shiga tsakani wajen neman sulhu.

Kara karanta wannan

'Dabarar da aka yi Katsina ta kawo karshen 'yan bindiga da kashi 70,' Gwamnati

Wasu 'yan bindiga yayin zaman sulhu a Katsina
Wasu 'yan bindiga yayin zaman sulhu a Katsina. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

BBC Hausa ta rahoto cewa hakan ya jawo ce-ce-ku-ce bayan da aka gano cewa 'yan ta'addan sun gabatar da wasu manyan buƙatu ga gwamnatin jihar domin a samu zaman lafiya.

Buƙatun da 'yan bindiga suka nema

Kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Nasiru Mu’azu, ya bayyana cewa ƴanbindiga sun miƙa buƙatu kamar haka:

1. Gina makarantu

2. Samar da asibitoci

3. Kafa mashayar dabbobi

Ya ce waɗannan buƙatu sun fito daga tattaunawar da aka yi domin samun hanyoyin da za su kawo ƙarshen hare-haren da suka addabi yankuna da dama.

A cewarsa, matsalar rashin abubuwan more rayuwa da kuma tsananin talauci a karkara na daga cikin tushen rikicin da ake fuskanta.

Rushewa sulhu da tasirinsa a Katsina

Mu’azu ya bayyana cewa rushewar shirin yafiya da gwamnatin Katsina ta yi a baya ya taimaka wajen faɗaɗa matsalar tsaro a jihar.

Ya ce daga ƙananan hukumomi biyar da matsalar ta taɓa shafa tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015, yanzu ta yaɗu zuwa ƙananan hukumomi 25 daga 2015 zuwa 2023.

Kara karanta wannan

Sulhu ya kankama, gwamna ya kawo shirin da za a tallafawa tubabbun 'yan bindiga

Sanarwar bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Katsina ta ce wannan rushewar ya ƙara bai wa ƴanbindiga ƙarfi wajen yawaita garkuwa da mutane da kai hare-hare.

Ra’ayin masana tsaro kan lamarin

Masani a fannin tsaro, Kabiru Adamu, ya bayyana cewa matakin amsa wasu buƙatun na iya taimakawa wajen rage rikice-rikice a Katsina.

Ya ce an sha zaluntar wasu daga cikin mutanen da suka shiga fashin daji, don haka idan aka ba su tallafi zai iya rage ƙiyayya da tashin hankali.

Sai dai ya yi gargadin cewa dole ne a yi tantancewa sosai, domin akwai daga cikinsu da suka ɗauki fashi da garkuwa da mutane a matsayin sana’a.

Gwamnati ta ce ta rage matsalar tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara a yaki da 'yan bindiga.

Kwamishinan tsaro na jihar Katsina ya bayyana cewa an shawo kan kashi 70 na matsalolin 'yan ta'adda a fadin jihar.

Bugu da kari, gwamnatin ta sanar da cewa an ceto daruruwan mutane daga wajen masu garkuwa da hallaka wasu daga cikin 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng