Noma: Mutane Miliyan 21 za Su Samu Ayyuka a Shirin da Gwamnati Ta Kawo
- Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin samar da sababbin manufofi a bangaren noma da za su iya samar da ayyukan yi miliyan 21 a Najeriya
- Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce an kaddamar da shirin ne domin inganta noma da rage dogaro da shigo da abinci
- Shirin ya hada da noman ban-ruwa, samar da bashi, kirkirar tsarin rajistar filaye, da kuma saka hannun jari a fannin noma na zamani
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana wasu shirye-shirye a bangaren noma da za su iya samar da ayyukan yi miliyan 21 tare da rage matsalar yunwa da hauhawar farashin abinci.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a taron da hukumar FAO ta shirya a Abuja.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai kan taron ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafin X na mataimakin shugaban kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce shirin zai taimaka wajen ciyar da manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu gaba, tare da tabbatar da cewa Najeriya ta rage dogaro da abinci daga kasashen waje.
Sabon shirin noma da aka kawo
Shettima ya bayyana cewa gwamnati za ta aiwatar da manyan shirye-shirye, ciki har da ban-ruwa a gonaki fiye da hekta miliyan 3.
Haka zalika za a ba manoma bashi da kuma kirkirar cibiyoyin rajistar filaye domin saukaka saka hannun jari.
Punch ta wallafa cewa Shettima ya ce Najeriya na iya noman ban-ruwa a sama da hekta miliyan uku, amma yanzu ana amfani da kasa da kashi 10 na hakan.
Mataimakin shugaban kasar ya yi nuni da cewa saka jari a ban-ruwa kadai zai iya ninka yawan amfanin gona sau uku, tare da rage radadin sauyin yanayi.

Source: Twitter
Bayanin ministan noman Najeriya
Ministan Noma Abubakar Kyari, ya ce Najeriya na da filaye masu faɗi, kasuwa mai girma, da yanayi mai kyau wanda ke bai wa masu saka hannun jari damar shiga harkokin noma.
Shi ma ministan kasafi, Sanata Atiku Bagudu, ya ce noma na da rawar da za ta taka wajen canza tsarin tattalin arzikin kasar, musamman idan aka mai da hankali a bangaren noman rani.
A nasa bangare, Ministan Noma da Kiwo na kasar Gambiya, Dr Demba Sabally, ya jinjinawa Najeriya kan ci gaban da ta samu a fannonin shinkafa da gero.
Kira ga gwamnatin Najeriya kan noma
Wakilin hukumar FAO a Najeriya da ECOWAS, Dr Hussein Gadain, ya ce shirin FAO na da burin tabbatar da ci gaban noma da bunkasa yankunan karkara.
Shugaban kungiyar manoma ta kasa (AFAN), Kabir Kebram, ya ce dole ne gwamnati ta tabbatar da cewa an aiwatar da dukkanin wadannan manufofi.
Haka zalika, shugaban masu noman shinkafa, Peter Dama, ya gargadi gwamnati da kada ta tsaya da alkawari kawai ba tare da aiki a aikace ba.
Manoma sun gargadi Bola Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa ana cigaba da samun korafi daga manoma yayin da gwamnatin Najeriya ta shigo da abinci.
Kungiyoyin manoma a Najeriya sun yi gargadi da cewa za a iya rasa masu samar da abinci a cikin gida idan aka cigaba da karya farashi.
Wani rahoto da Legit Hausa ta samu ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta kashe sama da Naira tiriliyan 2 wajen shigo da abinci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


