Babban Malamin Musulunci Ya Rasu a Najeriya, Pantami Ya Tuna Haɗuwarsu Ta karshe
- Al'ummar Najeriya sun shiga jimami bayan sanar da rasuwar babban limamin Musulunci a jihar Ondo wanda ya ba da gudunmawa sosai
- An tabbatar da rasuwar babban limamin Owo a Ondo, Sheikh Ahmad Aladesawe, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Limamai a jihar
- Sheikh Isa Ali Pantami ya tura sakon ta'aziyya ga iyalai da al'ummar Musulunci kan babban rashin da aka yi a Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Owo, Ondo - Najeriya ta shiga jimami bayan rasa babban malamin addinin Musulunci wanda ya ba da gudunmawa ga al'umma.
An tabbatar da rasuwar Sheikh Ahmad Aladesawe a jihar Ondo wanda kuma shi ne shugaban kungiyar limamai a jihar Ondo.

Source: Facebook
Pantami ya jajantawa iyalan malamin Musulunci
Farfesa Isa Ali Pantami ya tura sakon ta'aziyya ga al'ummar Musulmi da kuma iyalan marigayin a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Musulunci ya yi rashi: Daraktan agaji na kungiyar Izala, Alhaji Abdullahi ya rasu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Pantami ya ce ya yi matukar kaduwa da samun labarin rasuwar malamin wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin hidimar addini.
Sheikh Pantami ya ce:
"Mun samu labarin rasuwar babban limamin Owo, kuma shugaban kungiyar Limamai da Alfas na Ondo, Sheikh Ahmad Aladesawe, cikin bakin ciki da tawakkali.
"Rasuwarsa babban rashi ne ga iyalansa, mutanen Owo, jihar Ondo da ƙasa baki ɗaya. Ya kasance mutum na gaskiya da tawali’u.
"A madadin iyalina, ina mika ta’aziyyata ga dangi, al’ummar musulmi, jama’ar Owo da gwamnatin Ondo. Allah ya gafarta masa, ya karfafa iyalansa."

Source: Facebook
Wasu kyawawan halayen marigayin Pantami ya tuna?
Sheikh Pantami ya tuna haduwarsa ta karshe da fitaccen malamin a jihar Ondo yayin wani gagarumin taro da suka yi.
Tsohon ministan ya ce tabbas mutum ne mai saukin kai inda ya tuna yadda ya tarbe shi tare da yabon halayensa na kirki.
Ya kara da cewa:
"Ina iya tunawa da kyau, cike da jin dadi, ziyarata ta Owo a shekarar 2022, lokacin da jami'ar Achievers ta ba ni digirin girmamawa.
"Tsananin soyayya na mutanen wurin sun bayyana sosai ta hannun marigayi Babban Limami, wanda ya tsaya a matsayin mutum mai hikima
"Ya kasance mutum mai gaskiya da tawali’u, abin koyi ga al’umma, wanda rayuwarsa ta bar babban darasi ga musulmi da ma Najeriya baki ɗaya."
A karshe, Pantami ya yi addu'ar Allah ya yi masa rahama, ya saka masa da gidan aljannar firdausi tare da ba iyalansa hakurin jure wannan rashi.
An yi rashin malamin Musulunci a jihar Kano
Mun ba ku labarin cewa jihar Kano ta yi rashin babban malamin Musulunci, Sheikh Manzo Arzai, a ranar Lahadi 31 ga Agusta, 2025 da ta gabata.
Imam Muhammad Nur Muhammad Arzai ya sanar da lokacin jana’izar, inda ya ce za a yi sallar gawar marigayin da misalin karfe 2:30 na rana.
An tabbatar da cewa an gudanar da jana’izar marigayin a Zawiyar Sheikh Manzo Arzai da ke Unguwar Arzai a Kano, inda aka yi addu’ar Allah ya gafarta masa ya ba shi gidan aljanna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
