Dangote Ya Bayyana Abin da Matatarsa Ta Kawo Karshensa a Najeriya

Dangote Ya Bayyana Abin da Matatarsa Ta Kawo Karshensa a Najeriya

  • Aliko Dangote ya yi magana kan kalubalen da ya fuskanta wajen gina matatarsa da ke jihar Legas
  • Attajirin dan kasuwan ya ce ya fuskanci gargadi daga masana da jami'an gwamnati na cikin gida da na waje cewa irin wannan aikin ba kowa ke iya yinsa ba
  • Ya bayyana cewa fara samar da fetur daga matatar shekara guda da ta gabata ya kawo karshen shekaru 50 na yin dogon layin wajen samun mai a Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yi magana matatarsa.

Aliko Dangote ya bayyana cewa ya dauki babbar kasada wajen gina matatarsa da ke Legas.

Dangote ya fuskance kalubale wajen gina matatarsa
Hoton hamshakin attajiri, Aliko Dangote Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matatar Dangote ta shekara guda da fara samar da fetur

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa Dangote ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin, 15 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

Abin fashewa ya tarwatse a masana'antar sojojin Najeriya, an rasa rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shirya taron ne don murnar cika shekara daya da kaddamar da matatar mai karfin tace gangar mai 650,000 a rana.

Dangote ya bayyana cewa da a ce shirinsa na gina matatar bai yi nasara ba, da masu bada bashi sun kwace kadarorinsa.

Wane kalubale Dangote ya fuskanta

Da yake tuna kalubalen da ya fuskanta wajen gina matatar, Dangote ya bayyana cewa an dauki babbar kasada wajen tunkarar aikin.

Dangote ya ce kafin a fara aikin, masana, masu saka jari da jami’an gwamnati daga gida da waje, sun gargade shi cewa irin wannan aiki gwamnati kaɗai ce ke iya ɗaukar nauyinsa.

“Mun fuskanci ƙalubale domin burinmu shi ne mu sauya fasalin fannin harkai mai a Najeriya. Wasu sun yi zaton muna kokarin hana su samun na abinci, amma ba haka ba ne."
"Abin da muka yi shi ne mu sanya kasarmu da nahiyar Afrika su yi alfahari. A baya kasashen Afrika biyu ne kawai ba sa shigo da fetur, amma abin takaici yanzu sun koma shigo da shi. Hakan illa ne ga Afrika."

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Fubara ya fada kan Tinubu da Wike a jawabinsa na farko a Ribas

- Aliko Dangote

Dangote ya kawo sauki ga 'yan Najeriya

Dangote ya bayyana cewa tun da matatarsa ta fara samar da fetur shekara daya da ta gabata, aka kawo karshen matsalar yin dogon layi a gidajen mai, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da labarin.

Dangote ya yi magana kan matatarsa
Hoton matatar man Dangote da ke Legas Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya bayyana cewa tun daga shekarar 1975, ’yan Najeriya ke fama da dogayen layukan mai, amma hakan ya fara zama tarihi tun daga 15 ga Satumba, 2024 lokacin da matatar ta fara samar da fetur.

“Mun kwashe shekaru tun daga 1975 muna fama da dogayen layin mai, amma yau ’yan Najeriya suna cikin sabon zamani."

- Aliko Dangote

Idris Hussain Adam ya bayyanawa Legit Hausa cewa tabbas matatar Dangote ta kawo sauyi sosai a Najeriya.

"Layuka sun yi sauki a gidajen mai, domin yanzu akwai wadatarsa. Muna fatan dai fetur din ya yi arha sosai a kasuwa yadda mutane za su amfana."
"Ya kamata a ce ana sayansa da arha fiye da yadda farashinsa yake yanzu a kasuwa."

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta dakatar da hulda da wasu yan kasuwa a Najeriya, ta fadi dalilai

- Idris Hussain Adam

Matatar Dangote ta magantu kan raba fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote ta yi magana kan shirinta na rarraba mai kyauta zuwa sassan Najeriya.

Matatar ta bayyana cewa duk da korafin da wasu kungiyoyi a harkar mai ke yi, ba za ta fasa shirin da ta kudiri aniyar yi ba.

Hakazalika ta sanar da cewa tana sane da yunkurin da kungiyoyin su ke yi na kawo mata cikas, inda su ke fakewa da cewa suna kokarin 'yanta ma'aikata.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng