Najeriya Ta Rasa Babban Malamin Musulunci, Shugaban Limaman Ondo Ya Rasu

Najeriya Ta Rasa Babban Malamin Musulunci, Shugaban Limaman Ondo Ya Rasu

  • Babban limamin Owo Sheikh Ahmad Olagoke Aladesawe ya rasu yana da shekara 91 bayan hidima ga addini da al’umma
  • Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya mika ta’aziyya ga iyalai, musulmi da jama’ar jihar bisa wannan babban rashi
  • Rahotanni sun nuna cewa za a yi jana’izarsa yau Talata 16 ga Satumba 2025 da misalin ƙarfe 2:00 na rana a Owo, Ondo

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - An shiga jimami bayan rasuwar Sheikh (Dr) Imam Alhaji Mayor Ahmad Olagoke Aladesawe, babban limamin Owo a jihar Ondo yana da shekara 91.

An ce marigayin ya kasance shugaba kuma jagora ga musulmi a jihohi da dama, inda ya shahara wajen bayar da ilimi da kuma jagorancin al’umma cikin lumana.

Limamin Owo da ya rasu a jihar Ondo
Limamin Owo da ya rasu a jihar Ondo. Hoto: @LuckyAiyedatiwa
Source: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan rasuwar malamin ne a cikin wani sako da gwamna jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

An nuna fuskar Kachalla Babaro da ya kai hari masallaci, ya kashe Musulmai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoto ya ce marigayin ya shafe rayuwarsa wajen hidimar addini, abin da ya sa aka yaba masa a matsayin mutum mai gaskiya, nagarta da kuma kishin addini da ci gaban jama’a.

Rayuwar Sheikh Ahmad Aladesawe

Sheikh Aladesawe ya shahara a matsayin malami kuma tsohon babban malamin makaranta kafin ya zama babban limamin Owo.

Har zuwa rasuwarsa, ya kasance Sakataren janar na ƙungiyar limamai da malamai na Kudu maso Yamma da jihohin Edo da Delta, tare da rike shugabancin ƙungiyar a jihar Ondo.

An ce ya shahara wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da kuma kawo shawarwari ga shugabanni da mabiya addini.

Jana’iza da shirye-shiryen birne malamin

Daya daga cikin abokan marigayin, Alhaji Kamorudeen Ishola ya tabbatar da rasuwarsa ga manema labarai a Akure.

Baya ga haka, ya bayyana cewa za a gudanar da jana’izar marigayin yau Talata, 16 ga Satumba, da ƙarfe 2:00 na rana a unguwar Okeogun, kusa da makarantar Ansarudeen, Otapete, Owo.

Kara karanta wannan

Mutuwa mai yankar kauna: Matashin dan siyasa, Yunusa Yusuf ya rasu a Abuja

Haka kuma, sakataren janar na kungiyar malamai a jihar Ondo, Imam Abdulrasheed Akerele ya sanar da cewa dukkan shirye-shiryen jana’iza sun kammala.

Ta’aziyyar shugabanni da kungiyoyin Ondo

Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana cewa kodayake jama’a suna cikin alhini, akwai nutsuwa da kwanciyar hankali idan aka tuna cewa Sheikh Aladesawe ya yi rayuwa mai kyau.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kura-kuransa, ya ba shi Aljannar Firdausi.

Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa. Hoto: @LuckyAiyedatiwa
Source: Twitter

Haka nan, jagoran ƙungiyar NACOMYO a jihar Ondo, Abdulwaasii Yuusuf ya yi ta’aziyya ga iyalan marigayin da al’ummar Musulmi.

Abdulwaasii Yuusuf ya ce Malamin ya bar darussa na nagarta da kishin addini da za a ci gaba da tunawa da su.

An farmaki limamin Izala a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa wasu da ake zargi masu bikin Takutaha ne a jihar Kano sun kai hari a wani masallacin Izala.

Rahotanni sun tabbatar da cewa baya ga kona masallacin, maharan sun shiga gidan limamin tare da kona shi baki daya.

Shugaban kungiyar Izala na jihar ya yi kira ga rundunar 'yan sanda da hukumar DSS da su dauki matakin da ya kamata kan lamarin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng