Gwamna Ya Tsige Mai Martaba Sarki kan Rike Kujerun Sarauta 2
- Gwamna Bassey Otu ya tsige Ntufam Linus Oben Tabi daga sarautar Mbot Akpa da Ekinta a Akamkpa
- An zarge shi da karɓar takardar shaida ta bogi da kuma riƙe shugabanci a manyan yankuna biyu lokaci guda
- Gwamnatin jihar ta bayyana matakin a matsayin tabbatar da zaman lafiya da tsari a cikin al’ummomi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Cross River - Gwamnan Jihar Cross River, Bassey Otu, ya tsige Ntufam Linus Effiong Oben Tabi daga mukamin Sarkin Mbot Akpa da Ekinta a karamar hukumar Akamkpa.
Matakin ya biyo bayan zarge-zargen aikata ba daidai ba da suka haɗa da mallakar shaidar bogi da kuma yin amfani da mukamin shugabanci a wurare biyu lokaci guda.

Source: Twitter
Leadership ta wallafa cewa kwamitin kula da harkokin sarauta na jihar da ya yi bincike ya gano cewa Mbot Akpa ba ya cikin jerin ƙauyukan da doka ta amince da su tun daga 1996.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da aka gano game da Sarkin
Rahoton hukumar kula da sarauta ya nuna cewa Ntufam Tabi ya karɓi takardar shaida ta shugabanci ta ƙauyen Mbot Akpa da ta da ce ba.
Hakan na zuwa ne bayan gano cewa ba a amince da yankin ba a cikin dokar kafa yankuna ta 1996.
Haka kuma, an gano cewa Tabi ya riƙe shugabanci a yankuna biyu daban-daban da ke cikin ƙananan hukumomi biyu a jihar, abin da masu sukar sa suka kira da laifi da keta doka.
Wannan mataki na gwamna ya biyo bayan koke-koke daga shugabannin gargajiya guda biyar na majalisar Ekonganaku.
Bayanin gwamnati na cire Sarkin
Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin sarauta, Otuekong Francis Edet, ya tabbatar da tsige Tabi daga sarauta.
Ya yi magana yana mai cewa an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.
A cikin takardar tsige shi, gwamnati ta bayyana cewa Tobi ya samu shaidar da ya mallaka ne ta hanyar bogi, tare da ƙoƙarin yaudarar gwamnati da jama’a.

Source: Facebook
Takardar ta kuma nuna cewa ƙauyen Mbot Akpa da Tabi ya jingina kansa da shi daidai yake da Esuk Effiom Iyaweh da ke cikin Iko Eneyo a karamar hukumar Akpabuyo.
Martanin Mai martaba Ntufam Tabi
Duk da wannan mataki, Ntufam Tabi ya bayyana cewa bai da abin cewa a yanzu, domin har yanzu bai karɓi takardar tsige shi ba daga gwamnati.
A cewarsa, idan aka miƙa masa takarda kuma doka ta tabbatar da matakin, zai karɓa ba tare da matsala ba.
Sai dai kuma ya ce idan aka gano cewa doka ba ta amince da tsige shi ba, zai ɗauki matakin da ya dace wajen kare kansa da mukaminsa.
An gyara dokar sarauta a Adamawa
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Adamawa ta yi wa wasu dokokin da suka shafi sarauta kwaskwarima.
Dokokin da aka yi wa gyara za su ba gwamnatin jihar damar sauke sarkin da ya gaza jagorantar masarautar shi saboda rashin lafiya.
Tun a kwanakin baya dai gwamnan jihar Adamawa ya kawo wasu sauye sauye a kan masarautar jihar da suka shafi sarakuna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

