Shugaba Tinubu Ya Yanke Hutunsa, Ya Sanya Lokacin Dawowa Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Yanke Hutunsa, Ya Sanya Lokacin Dawowa Najeriya

  • Hutun da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya je yi a kasar waje ya zo karshe, inda ya shirya dawowa gida Najeriya
  • Tinubu ya kammala hutunsa kafin lokacin da aka tsara a cewar wata sanarwa da hadiminsa ya fitar a ranar Litinin, 15 ga watan Satumban 2025
  • Mai girma Tinubu zai dawo Najeriya domin dorawa kan inda aka tsaya wajen gudanar da harkokin gwamnati

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya kammala hutun aikinsa da ya je yi a kasar Faransa.

Shugaba Tinubu zai dawo babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 16 ga watan Satumban 2025, domin ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati.

Shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya
Hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na X, a ranar Litinin, 15 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

Bayan shekara 2, Gbajabiamila ya haska wani dalilin Tinubu na cire tallafin fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da Bola Tinubu ya tafi hutu

Shugaba Tinubu ya bar Najeriya a ranar 4 ga watan Satumba zuwa ƙasar Faransa a wani ɓangare na hutunsa na shekara.

Tun da farko ya yi niyyar raba lokacin hutun nasa tsakanin kasashen Faransa da Birtaniya (UK).

A makon da ya gabata lokacin da yake birnin Paris, Shugaba Tinubu ya yi liyafar sirri tare da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a fadar Élysée.

Shugabannin kasashen biyu sun tattauna kan muhimman fannoni na haɗin gwiwar kasashensu tare da amincewa da karfafa dangantaka domin bunkasa juna da tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya

A cikin sanarwar da Bayo Onanuga, ya fitar, ya bayyana cewa Tinubu zai dawo Najeriya a ranar Talata, 16 ga watan Satumban 2025.

"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala hutun aikinsa kafin lokacin da aka tsara, kuma zai dawo Abuja a ranar Talata, 16 ga watan Satumba, 2025, domin ci gaba da ayyukan gwamnati."

Kara karanta wannan

Tsohon soja zai bada wuri, Simi Fubara zai koma kujerar gwamnan Rivers

"Shugaban kasan ya tafi Faransa a ranar 4 ga Satumba, 2025, domin shafe wani ɓangare na hutunsa na shekara, kuma tun farko an tsara ya raba hutun tsakanin kasashen Faransa da Birtaniya.”

- Bayo Onanuga

Shugaba Tinubu ya kammala hutu
Hoton shugaban kasa Bola Tinubu yana jawabi Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Karanta wasu labaran kan Shugaba Tinubu

Majiya ta magantu kan takarar Tinubu da Shettima

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu bayani daga wata majiya a fadar shugaban kasa, kan bullar jita-jitar da ke cewa Mai girma Bola Tinubu, zai ajiya Kashim Shettima gabanin zaben 2027.

Wani amintacce a fadar shugaban kasa ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a rade-radin, amma a jira lokaci domin shi ne kawai zai warware komai.

Majiyar ta kara da cewa shugaban kasan bai taba tattaunawa da kowa ba kan batun maye gurbin Shettima a 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng