An Kara Samun Sauki da Farashin Abinci da Wasu Kayayyaki Ya Sauka a Najeriya
- Hukumar Kididdiga ta Kasa watau NBS ta tabbatar da cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu a watan Agusta, 2025
- A wani rahoton NBS ta fitar yau Litinin, 15 ga watan Satumba, 2025, ta ce hauhawar farashin kaya ya sauka zuwa 20.12% a watan jiya
- Rahotan ya danganta wannan sauki da aka samu da saukar farashin shinkafa, gero, dawa, garin masara da wasu kayan amfani na yau da kullum
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya sauka zuwa 20.12% a watan Agustan da ya gabata a 2025.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ce ta bayyana hakan yayin da ta fitar da alkaluman hauhawar farashin kayayyaki na wata-wata da ta saba fitarwa.

Source: UGC
Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa da hauhawar farashin abinci ma ya ragu da 1.65%, idan aka kwatanta da 3.12% da aka samu a watan Yuli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ya kawo saukar farashin kaya a Najeriya?
Wannan saukar, in ji rahoton, ya samo asali ne daga raguwar farashin shinkafa (sakamakon shigo da ita daga waje), garin dawa, garin masara, dawa, gero, semovita, madarar waken suya da sauransu.
Rahoton ya bayyana cewa alkaluman watan Agusta, 2025 sun nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ya sauka da 1.76% idan aka kwatanta da 21.88% da aka samu a watan Yuli.
"A kididdigar shekara-shekara, hauhawar farashin kaya ya dawo 12.03% ƙasa da wanda aka samu a watan Agusta 2024 (32.15%).
"Wannan ya nuna cewa hauhawar farashin kaya na shekara zuwa shekara ya ragu a watan Agusta 2025 idan aka kwatanta da watan Agusta 2024," in ji MBS.
Yadda farashin kayan abinci ya sauka
Rahoton ya ƙara da cewa hauhawar farashin abinci na shekara-shekara a watan Agusta 2025 ya tsaya a 21.87%, wanda ya yi ƙasa da 15.65% idan aka kwatanta da watan Agusta 2024 (37.52%).
A kididdigar wata zuwa wata kuwa, farashin abinci ya sauka zuwa 1.65%, ƙasa da 3.12% na watan Yuli 2025, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Source: Getty Images
A ƙarshe, rahoton ya ce matsakaicin farashin abinci a cikin watanni 12 da suka kare a watan Agusta 2025 ya kasance 25.75%, wanda ya yi ƙasa da 11.24% idan aka kwatanta da wanda aka samu a watan Agusta 2024 (36.99%).
Wannan rahoto da hukumar NBS ta fitar ya nuna saukin da aka samu a farashin kayan abinci irinsu shinkafa da sauran kayayyaki, wanda ke tasiri matuka ga talakawan Najeriya.
Yadda Tinubu ya karya farashin abinci
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta jaddada cewa tana ci gaba da daukar matakan da suka dace domin karya farashin abinci a kasar nan.
Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari, ya ce matakan gaggawa da Shugaba Tinubu ya ɗauka tun a 2023 kan abinci sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Sanata Kyari ya tabbatar da cewa farashin abinci ya ragu sosai a kasuwannin Najeriya saboda matakin da aka dauka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

