An Nuna Fuskar Kachalla Babaro da Ya kai Hari Masallaci, Ya Kashe Musulmai

An Nuna Fuskar Kachalla Babaro da Ya kai Hari Masallaci, Ya Kashe Musulmai

  • An bayyana fuskar shugaban ƴan bindiga Babaro wanda ake zargi da kai hari a Masallacin Mantau da ya hallaka mutane 32
  • Rahotanni sun ce Babaro ya bayyana a wani taron tattaunawa da zaman lafiya a Faskari yayin da ake masa zargi da kai hare-hare
  • Bayan harin, gwamnatin Katsina ta tura tawaga ta musamman don yin ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Katsina - Wani hoto da ya bayyana ya nuna fuskar shugaban ƴan bindiga Babaro, wanda ake zargi da kai harin da ya hallaka mutum 32 a Masallacin Mantau a Malumfashi, jihar Katsina.

Harin da aka ce an kai shi yayin da ake gudanar da sallar asuba, ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da tashin hankali.

Kara karanta wannan

Sa'o'i da sulhu, 'yan bindiga sun rufe masallaci, sun sace masu sallah 40 da Asuba

Kachalla Babaro yayin zaman sulhu da aka yi a Katsina
Kachalla Babaro yayin zaman sulhu da aka yi a Katsina. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ne ya wallafa hoton Kachalla Babaro a wani sako da ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babaro da aka fi sani da jagorantar hare-hare a Kankara da Malumfashi, ya halarci wani taron zaman lafiya a Faskari a ranar Lahadi duk da irin zarge-zargen da ake masa.

Harin da Kacahalla Babaro ya kai masallaci

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindiga sun afka cikin masallacin ne misalin ƙarfe 5:00 na safe a watan Agustan 2025, inda suka bude wuta kan masu ibada.

Lamarin ya jawo mutuwar mutum 32, yayin da wasu da dama suka jikkata kuma wasu suka tsere cikin firgici domin tsira da rayukansu.

A cewar jami’an tsaro, harin na ramuwar gayya ne da ƴan ta’addan suka shirya kan al’ummar yankin.

Kacahalla Babaro ya sace mutane bayan harin

Bayan aukuwar lamarin, an ruwaito cewa wasu daga cikin mazauna garin sun shiga hannun masu garkuwa, sai dai rundunar sojin sama ta Najeriya ta kai dauki.

Kara karanta wannan

Mauludi: Masu Takutaha sun kona masallacin Izala da gidan liman a Kano

Punch ta wallafa cewa daukin ya tarwatsa ƴan bindigan tare da kubutar da wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su, yayin da sauran suka gudu cikin rudani.

Wasu daga cikin waɗanda suka tsira yanzu haka suna karɓar magani a asibitoci daban-daban a cikin jihar.

Dan bindiga Ado Aliero yayin taron sulhu a Katsina
Dan bindiga Ado Aliero yayin taron sulhu a Katsina. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

A lokacin, gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda, ya umurci mataimakinsa Mallam Faruk Jobe da ya tura tawaga ta musamman don jajanta wa iyalan da abin ya shafa.

Barazanar Kachalla Babaro a Katsina

Babaro, wanda aka fi danganta shi da kai hare-hare a Kankara da Malumfashi, ya ci gaba da zama babban barazana ga al’ummar Katsina.

Rahoto ya nuna cewa kasancewarsa a wani taron tattaunawa da zaman lafiya a Faskari ya fara kwantar da hankalin mazauna kauyukan da ya addaba.

Ado Aliero ya ce za a zauna lafiya

A wani rahoton, kun ji cewa kasurgumin dan bindiga, Ado Aliero ya halarci taron sulhu da aka shirya a yankin Faskari na jihar Katsina.

A cikin jawabin da ya yi, dan ta'addan ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar cewa za a samu zaman lafiya a yanzu.

Kara karanta wannan

Isiya: Hatsabibin ɗan bindiga da ake nema ya miƙa wuya ga zaman lafiya a Katsina

Ya kara da cewa a kwanakin baya an kulla yarjejeniya da shi amma ya warware ta bayan kama dan shi da hukuma ta yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng