Gwamna Radda Ya Fadi Dalilin Kasa Fara Aikin Titin N18.9bn da Ya Yi Alkawari
- Gwamna Dikko Umaru Radda ya taba batun rashin fara aikin titin Katsina–Sabuwa wanda zai lakume N18.9bn
- Gwamnati ta riga ta fitar da N7.5bn don kaddamar da aikin, amma matsalar tsaro ta hana fara shi
- Sai dai, Gwamna Radda ya nuna kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba za a fara aikin idan zaman lafiya ya dawo a yankin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina – Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan dalilin kasa fara aikin titin Katsina-Sabuwa, wanda zai lakume Naira biliyan 18.9.
Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ce ta sanya ba a fara aikin titin ba har zuwa yanzu.

Source: Facebook
Babban sakataren yada labaran gwamnan Katsina, Ibrahima Kaulaha Mohammed, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook.
Wane jawabi Gwamna Radda ya yi?
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi wata tawaga da ta hada da dattawa, Hakimai, shugabannin 'yan kasuwa, malamai, 'yan siyasa, matasa da sauran masu ruwa da tsaki daga karamar hukumar Sabuwa.
Titin mai tsawon kilomita 27 zai hada garin Sabuwa da Tashar Bawa, tare da ratsawa cikin akalla kauyuka 13.
Gwamna Radda, yayin ganawa da shugabannin al’umman, ya ce gwamnati ta riga ta fitar da N7.5bn, wato kaso 40% cikin 100% na kudin aikin, domin farawa amma rashin tsaro a yankin ya hana 'yan kwangila shiga.
"Da zarar an dawo da zaman lafiya, 'yan kwangila za su shiga da kwarin gwiwa domin tabbatar da kammala aikin cikin lokaci."
- Gwamna Dikko Umaru Radda
Gwamna Dikko Radda ya nuna kwarin gwiwa kan cewa duba da yunkurin sulhu da 'yan bindiga da ake yi a yankin, nan ba da jimawa ba za a fara aikin.
Tattaunawa da ’yan bindiga
Dan majalisar jiha mai wakiltar Sabuwa, Hon. Danjuma Ibrahim, ya bayyana cewa wasu kungiyoyin 'yan bindiga sun nuna sha’awar shiga tattaunawar sulhu da al’ummar yankin.
Ya ce ma’aikatar tsaron cikin gida na aiki da tsarin da zai taimaka wajen tabbatar da tattaunawar.

Source: Facebook
Karin martani daga shugabanni
Injiniya Tasiu Abubakar ya yaba da kokarin gwamnati na sanya ’yan asalin yankin a cikin gwamnati da kuma amincewa da muhimman ayyuka a Sabuwa.
Ya kuma bukaci a farfado da filin aikin gona na gwamnatin tarayya a yankin domin karfafa samar da abinci da samar da ayyukan yi.
Shugaban karamar hukumar Sabuwa, Sagir Tanimu, ya ce kudin da gwamnatin jiha ta saki, sun taimaka wajen aiwatar da kananan ayyuka da suka farfado da harkokin kasuwanci da samar da guraben ayyukan yi.o
Gwamna Radda ya magantu kan ilmi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa ilmi babban makami ne na yaki da matsalar rashin tsaro.
Gwamna Radda ya bayyana cewa da ilmi ne za a samu damar magance matsalar rashin tsaro tun daga tushenta.
Ya bayyana cewa ilmi mai inganci yana taka muhimmiyar rawa wajen yaki da ta'addanci ta hanyar rage talauci da jahilci.
Asali: Legit.ng

