Ambaliya Ta Lalata Gonaki da Gidaje bayan Mamakon Ruwan Sama a Kaduna

Ambaliya Ta Lalata Gonaki da Gidaje bayan Mamakon Ruwan Sama a Kaduna

  • Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da gonaki a garin Manchok, da ke masarautar Moro’a a karamar hukar Kaura ta jihar Kaduna
  • Mazauna yankin wadanda su ka rasa kayayyakin gida da amfanin gona, sun nemi agajin gaggawa daga wajen gwamnati
  • Lamarin wanda ya jawo asarar dukiya da amfanin gona, ya sanya mazaunan yankin sun mika kokon bararsu ga gwamnati

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Ambaliyar ruwa ta yi barna a garin Manchok da ke masarautar Moro’a ta karamar hukumar Kaura, a jihar Kaduna.

Mazauna garin sun roki gwamnatin tarayya da ta jiha da su kawo agajin gaggawa bayan ambaliyar ruwa mai tsanani da ta shafe gidaje da gonaki.

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje a Kaduna
Hoton wasu gidaje da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Kaduna Hoto: Ahmed Ali
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ambaliyar ruwan ta auku bayan an kwashe kwanaki uku ana mamakon ruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ruwan sama ya jawo ambaliya a Kaduna

Kara karanta wannan

'Za a sheƙa ruwa na kwana 5,' An faɗi jihohin Arewa 10 da za su gamu da ambaliya

Ruwan saman kamar da bakin kwarya ya haifar da ambaliyar da ta lalata gonaki, amfanin gona, da gidaje, inda jama’a suka shiga halin rudani.

Wani mazaunin garin da ruwan sama ya mamaye masa gida, Duniya Awuwu Sambo, ya shaida wa manema labarai cewa ambaliyar ta tarwatsa kayayyakin gidansa, ciki har da lantarki, kujeru, da sauran kayan gida.

“Ruwan ya lalata mini dukiya, ya kuma hana iyalina barci inda muka kwashe dare muna fitar da ruwa daga cikin gida."

- Duniya Awuwu Sambo

Haka kuma wani manomi, Luka Ishaya, ya bayyana cewa dukkan kayan gonakinsa wadanda sune hanyar sun abincinsa sun salwanta, sakamakon ambaliyar ruwan.

“Wannan ruwan sama maimakon ya amfane mu, sai ya jawo mana masifa. Abin bakin ciki ne sosai.”

- Luka Ishaya

Dalilan da suka haddasa ambaliyar

Wani mazaunin garin, Thomas Yatai, ya danganta ambaliyar da rufewar hanyoyin ruwa da kuma rashin ingantattun magudanan ruwa.

Ya kuma ce sakacin jama’a na zubar da shara a gefen tituna da cikin kwatami ya taimaka wajen toshe hanyoyin ruwa.

Shugaban matasan yankin, Moses Mathew, ya ce da ace magudanan ruwa suna aiki yadda ya kamata, da za a iya rage illar wannan bala’i.

Kara karanta wannan

Tawagar kasar Rasha ta dura Najeriya, ta sauka a jihar Neja

Ya bayyana cewa matasa sun yanke shawarar fara daukar matakan kai-da-kai ta hanyar samar da hanyoyin ruwa na wucin gadi da kuma share kwatami, yayin da suke jiran taimakon gwamnati.

Ambaliya ta yi barna a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan ambaliyar ruwa

Ambaliyar ruwa ta kashe rayuka a Zariya

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu asarar rayuka sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.

Ambaliyar ruwan wadda ta auku a yankin Tudun Jukun, ta yi sanadiyyar rasuwar akalla mutane guda uku har lahira.

Shaigun ganau ba jiyau ba, sun bayyana cewa mutanen da lamarin ya ritsa da su, sun rasa rayukansu ne lokacin da su ke kokarin ketara magudanan ruwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng