Akwai Kura: Matasan Arewa Sun Taso El Rufai a Gaba, an Ji Dalili

Akwai Kura: Matasan Arewa Sun Taso El Rufai a Gaba, an Ji Dalili

  • Kungiyar matasan Arewa ta 'Northern Youth Frontiers' ta bukaci tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya amsa tambayoyi kan zargin karkatar da kudaden
  • Ta bayyana cewa kin amincewa a bincike shi, na iya zama misali mara kyau ga shugabannin da su ka biyo bayansa
  • Kungiyar ta tunatar da El-Rufai cewa shugabanci amana ce kuma lallai ne a yi hisabi bayan kammala mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna – Kungiyar matasan Arewa mai suna 'Northern Youth Frontiers' ta taso tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaba.

Kungiyar matasan ta bukaci Nasir El-Rufai da ya mika kansa don a gudanar da bincike kan zargin karkatar da kudaden jihar a lokacin da yake mulki.

Matasan Arewa na son a binciki El-Rufai
Hoton tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Sama Musa, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Kungiyar dattawan Arewa ta samo.mafita ga gwamninin yankin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan Arewa sun yi zargi kan El-Rufai

Kungiyar ta yi zargin cewa El-Rufai ya ki mika kansa don a binciki yadda ya gudanar da mulkin jihar Kaduna.

Ta bayyana cewa kin amincewa a bincike shi kamar yadda ake zargi, zai iya lalata dimokuradiyya da kuma raunana gaskiya da adalci a shugabanci.

"Mulki amana ce. Duk wanda ya rike mukamin gwamnati ya wajaba ya kasance mai gaskiya da rikon amana. Mutanen Kaduna da ma ’yan Najeriya gaba daya na da hakkin sanin yadda aka tafiyar da dukiyarsu."

- Sama Musa.

Kungiyar ta ce abin takaici ne ganin wanda ya taba yin ikirarin gwamnatinsa ta dogara da gaskiya yanzu yana kaucewa a bincike shi, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar da labarin.

"Wannan hali ba kawai yana haifar da tambayoyi kan yadda ya tafiyar da mulkinsa ba, har ma yana iya kafa mummunan misali ga shugabannin da za su zo nan gaba."

Kara karanta wannan

'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki

- Sama Musa

An tono kalaman El-Rufai na baya

Kungiyar ta kuma tunatar da kalaman El-Rufai na cewa rundunar tsaronsa ta fi karfin ’yan sanda a lokacin mulkinsa, abin da ya jawo tambayoyi kan yadda ake amfani da kudaden jiha da kuma illarsa ga tsaron jama’a.

Matasan Arewa sun taso El-Rufai a gaba
Hoton tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Baya ga haka, kungiyar ta nuna damuwa kan zargin cewa ya taba biyan kudin fansa da kuma kai kayan abinci ga ’yan bindiga a lokacin mulkinsa.

"Wannan lamari abu ne mai tayar da hankali, domin yana nuna cewa gwamnati ta iya yin sulhu da masu tada kayar baya maimakon kare al’umma. Wannan ya jefa tsaro cikin hadari tare da tura sakon da bai dace ba."

- Sama Musa

Satguru Maharaj Ji ya kalubalanci El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa Satguru Maharaj Ji ya yi kakkausar suka ga Nasir El-Rufai, kan caccakar da yake yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan Tambuwal ya zargi Tinubu da shirin ruguza 'yan adawa

Satguru Maharaj Ji ya kalubalanci taohon gwamnan na Kaduna kan ya fito bainar jama'a ya yi rantsuwa cewa bai taba cim dukiyar.da aka ba shi amana ba.

Hakazalika, ya nuna goyon bayansa ga Shugaba Tinubu, inda ya bayyana cewa yana kokarin ganin ya gyara Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng