Sawun Giwa: Gwamna Ya Sauya Shawara bayan Barazanar Maka Shi a Kotu
- Bayan yi masa barazanar maka shi a kotu, Gwamnan Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya janye matakin da ya dauka a farko
- Gwamnan ya soke toshewar da ya yi wa lauya Festus Ogun a X, bayan ganawa da shi a fadar gwamnatin jihar Lagos
- Festus Ogun ya bayyana cewa Sanwo-Olu ya gayyace shi domin tattauna korafinsa kan tauye hakki, inda suka yi yarjejeniya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya gana da lauyan da ya yi barazanar maka shi a kotu.
Gwamna ya soke toshewar da ya yi wa lauya Festus Ogun a X, bayan ganawa da shi a fadar gwamnati.

Source: Twitter
Lauya ya gana da gwamna bayan barazanar kotu
Lauyan wanda ya taba zargin gwamnan da tauye hakki, ya sanar da wannan ci gaban a shafinsa na X ranar Asabar, inda ya yi rubutu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun ce an yi ganawar a fadar gwamnatin jihar Lagos domin tattauna wasu batutuwa da suka shafi kare hakkin dan Adam.
Ogun ya ce:
“Sanwo-Olu ya gayyace ni don tattauna korafina kan tauye hakki. Zamu ci gaba da rike gwamnati da gaskiya. Aluta continua!”
Rahoto ya nuna cewa Ogun ya kai karar Sanwo-Olu a kotu bisa zargin tauye hakki, bayan ya toshe shi a shafinsa na X.
A cikin karar, Ogun ya bayyana cewa an toshe shi saboda suka da bukatar hakki kan kisan #EndSARS a watan Oktoba, shekara ta 2020.
Ogun ya ce toshewar ta hana shi samun bayanan gwamnati, yana mai cewa hakan tauye hakkin samun bayanai ne bisa doka da tsarin mulki.

Source: UGC
Mutane sun tofa albarkacin bakinsu
Mutane da dama sun bayyana lauyan a matsayin mai karfin hali bayan barazanar maka gwamana sukutum da guda a kotu.
Mafi yawan mutane sun yaba masa kan karfin hali yayin da wasu ke yi masa shagube da cewa yana neman suna ne kawai.
Kikolme Sowore:
"Ya kamata ya biya ka kudi na musamman sabda bata maka lokaci da ya yi wanda kuma ka yi rashin wasu bayanai daga matakin jiha.
"Musamman badakalar da ke cikin gyaran babbar gadan 'Third Mainland' da ake zargin badakala sosai."
Bleh:
"Ko kadan ban yarda ba."
James Chinnel:
"Ba zan yi mamaki ba idan nan gaba ka fara yabonsa saboda wannan zama da kuka yi a Lagos."
Peaceful Revolution:
"Ya kamata hukumar INEC da ta toshe wasu ta shirya saboda ita ma za a iya maka ta a kotu."
Lauya zai maka gwamna a kotu
Mun ba ku labarin cewa wani lauya 'dan Najeriya ya nuna karfin hali bayan maka gwamna a kotu wanda ya jawo maganganu a kafofin sadarwa ta zamani.
Lauya Festus Ogun ya shigar da kara kan Gwamna Babajide Sanwo-Olu saboda ya toshe shi a manhajar X da aka fi sani da Twitter.

Kara karanta wannan
Maganar N Power ta dawo, Abba Hikima, Ɗan Bello za su koma kotu da gwamnatin Tinubu
Ogun ya ce ya sha wahala saboda matakin, amma bai nemi diyyar kudi ba domin ka da a dauke shi a matsayin mai neman riba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

