Abubuwan da Omoyele Sowore Ya Bankado game da Gwamnonin Arewa

Abubuwan da Omoyele Sowore Ya Bankado game da Gwamnonin Arewa

  • Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore na daga cikin matasa masu jajircewa wajen fadin gaskiya, inda yake ci gaba da sukar gwamnatoci
  • A kwanakin nan, ya kira Bola Tinubu babban mai laifi a Brazil, lamarin da ya sa DSS ta bukaci ya goge rubutunsa cikin awa 24
  • Duk da haka, Sowore ya ce babu wanda ya isa ya tilasta shi, inda ya cigaba da sukar gwamnoni irin su Babagana Zulum, Inuwa yaha da Agbu Kefas

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore na daga cikin matasa da ke nuna rashin tsoro wurin tabbatar da cewa sun fadi gaskiya komai dacinta.

Sowore ya sha arangama da jami'an tsaro kuma har yanzu yana kan ci gaba da takun-saka da sukar babban sufetan yan sanda, Kayode Egbetokun.

Sowore ya bankado wasu abubuwa game da gwamnonin Arewa
Gwamna Babagana Zulum, dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da Gwamna Inuwa Yahaya. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum, Omoyele Sowore, Muhammadu Inuwa Yahaya.
Source: Facebook

Abin da ya hada DSS da Sowore kan Tinubu

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Abba Hikima, Ɗan Bello za su koma kotu da gwamnatin Tinubu

Har ila yau, Sowore na yawan sukar gwamnatin Bola Tinubu ta kowane bangare da yake ganin an saba ka'ida ko kuma ba a yi adalci ba, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kwanakin nan, ya yi rubutu inda yake sukar Tinubu da kuma kiransa babban mai laifi yayin da yake ziyara a kasar Brazil.

Dalilin haka, hukumar DSS ta rubuta wasika da manhajar X tana neman ta tilasta shi godo rubutun da ya cikin awa 24.

Sai dai Sowore, ya sake rubutu a shafin X inda ce babu wanda ya isa ya sanya shi goge wannan rubutu, hasalima, yanzu ya fara har sai an samu shugabancin nagari.

Bayan haka, akwai wasu gwamnonin Arewa da Sowore ya taba kan zargin rashin yin katabus a wasu bangarori a jihohinsu.

Daga cikin gwamnonin akwai Babagana Umara Zulum na jihar Borno, Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe da Agbu Kefas na Taraba.

1. Zulum: Zarge-zargen Sowore kan gwamnatin Borno

Omoyele Sowore ya rubuta a shafukan sada zumunta har da Facebook cewa Gwamna Babagana Zulum yana gudanar da ɗakin azabtarwa da ake kira “The Crack FC” a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Aikin titi: Gwamnatin Tinubu za ta kashe Naira tiriliyan 3 a jihohin Arewa 2

A cewarsa, an tsare wasu matasa da suka yi zanga-zangar #EndBadGovernance a wannan wuri tsawon shekara guda, haka kuma ya zargi gwamnan da tsare ƙananan yara kan shiga zanga-zanga, yayin da ake ware biliyoyin kuɗi ga tubabbun yan Boko Haram.

Sowore ya bayyana cewa abin kunya ne yadda ake ba tsofaffin ’yan Boko Haram tallafi, amma matasa da ke neman shugabanci nagari ake tsarewa.

Martanin Zulum ga zarge-zargen Sowore

Sai dai gwamnatin jihar Borno ta karyata zarge-zargen Sowore inda ta nuna damuwa kan yada karya ba tare da bincike ba.

Kakakin gwamnan, Abdurrahman Bundi ya bayyana cewa waɗannan zarge-zargen ba su da tushe, kuma an yi su ne domin yaudarar jama’a.

Ya ce zanga-zangar #EndBadGovernance ma ta shafi gwamnatin tarayya ne, ba gwamnatin Borno ba.

Ya ƙara da cewa shirin DRR, wato sake tunani, gyara da dawo da tsofaffin yan Boko Haram yana da manufar taimaka wa waɗanda rikicin ya shafa.

Zarge-zargen Sowore kan gwamna Zulum
Gwamna Babagana Zulum da Omooyele Sowore. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum, Omoyele Sowore.
Source: Facebook

2. Inuwa: Zargin Sowore kan gwamnatin Gombe

Har ila yau, bayan sukar Gwamna Zulum, Sowore ya dawo kan takwaransa da jihar Gombe kan abin da ya kira wasa da harkar lafiya, kamar yadda ya fada a Facebook.

Kara karanta wannan

Soyinka: Yadda aka sace babban marubucin Najeriya a kasar waje, aka yi masa fashi

Sowore ya dauki wasu hotuna da asibitoci da ke nuna suna cikin wani hali da bai kamata ana amfani da su ba.

Bangaroron da Sowore ya fi tabawa a Gombe shi ne na lafiya da kuma shari'a inda ya ce Inuwa ya lalata komai bayan hawa mulki.

Daga bisani ya zargi gwamnan da neman yin barazana wurin amfani da yan dabar siyasa domin rufe bakin masu neman kawo sauyi a jihar.

Sai dai kuma a bangaren gwamnati, binciken Legit Hausa ya gano babu martani a hukumance sai dai daidaiku masoyan gwamnan da ke martani domin kare mai gidansu.

Abubuwan da Sowore ke zargi kan gwamna Inuwa a Gombe
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe yayin taro. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Source: UGC

3. Kefas: Zargin da Sowore ke yi kan gwamnatin Taraba

Omoyele Sowore ya kuma dura kan gwamnatin jihar Taraba musamman a bangarorin ilimi da kuma hanyoyi.

A wani rubutu da ya yi a Facebook, Sowore ya ce bai kamata a zabi Agbu Kefas a matsayin gwamnan jihar Taraba ba.

Ya ce:

"Tun farkon fari, bai kamata a ce Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas ya zama gwamna ba SAM SAM.

Kara karanta wannan

Meya sa rubutun Sowore ya fusata DSS? Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani

"Ya zama bala'i, sai ka ce tirelar da bata da birki da duk abin da ya sha gabanta murƙushewa take, ya jefa Taraba cikin bala'in da Allah ne kawai ya san irin girman ta'adin da ya yi."

Sowore ya tabo batun ilimi da kuma ruwan sha inda ya ce abin kunya ne samun irin wannan yanayi a zamanin nan.

Ya ce halin da Ilimin Jihar Taraba ya ke a 2025, ya yi kama da na 1945, har yanzu ɗaliban suna rubuta jarabawa a ƙasa yayin da aka sace biliyoyin Naira, an yi watsi da yara.

Sowore ya dura kan gwamnan Taraba
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba a Najeriya. Hoto: Agbu Kefas.
Source: Twitter

Sowore ya bukaci su hadu da Tinubu a kotu

A baya, kun ji cewa wani lauya ya soki bukatar DSS ta rufe shafin Facebook Omoyele Sowore, yana mai cewa hakan ya saba wa doka.

Ya ce wannan mataki na iya zama barazana ga ‘yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulki ya tanada.

Lauyan ya roki Meta da ka da ya amince da bukatar DSS domin kauce wa kafa mummunan tarihi a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.