Da Yiwuwar a Tsige Sarki, Gwamna Ya Dauki Mataki kan Abin Kunyar da Mai Martaba Ya Yi

Da Yiwuwar a Tsige Sarki, Gwamna Ya Dauki Mataki kan Abin Kunyar da Mai Martaba Ya Yi

  • Da yiwuwar za a tsige Sarkin Ipetumodu ko akasin haka a jihar Osun bayan hukuncin daurin da aka yanke masa a Amurka
  • A karon farko tun bayan daure Sarkin, Gwamna Adeleke ya ba da umarnin daukar mataki kan halin da masarautar Ipetumodu ta tsinci kanta
  • Wannan na zuwa ne bayan an fara samun sabani tsakanin masarauta da masu zaben Sarki kan batun maye gurbin mai martaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun - Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana rashin jin dadi game da halin da al'ummar Ipetumodu da ke karamar hukumar Ife ta Arewa ke ciki bayan daure Sarkinsu a Amurka.

A kwanakin baya ne kotun Amurka ta daure Sarkin Ipetumodu, Mai Martaba Joseph Oloyede, (Apetu na Ipetumodu) a gidan yari na tsawon watanni 56.

Kara karanta wannan

A karshe, Kotun Abuja ta yanke hukunci kan shugaban Ansaru da aka cafke

Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun.
Hoton gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke a dakin taron gidan gwamnati Hoto: Ademola Adeleke
Source: Facebook

Jaridar Tribune Nigeria ta tattaro cewa an daure Sarkin ne bisa laifin cin kudin tallafin COVID-19 har Dala miliyan 4.2 tare da yin rajistar takardun haraji na bogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikici ya barke bayan daure Sarki a Amurka

Bayan wannan hukuncin, Ipetumodu, wadda ita ce cibiyar karamar hukumar Ife-North, ta koma tamkar babu Sarki, wanda hakan ya haifar da rikici tsakanin masarautar da kuma masu zaben sarki.

An ruwaito cewa kan masu zaben sarki a Ipetumodu ya rabu biyu game da yadda za a maye gurbin Oba Oloyede.

Wasu daga cikinsu ba su yarda da tsige sarkin ba, suna fatan zai dawo daga kurkuku ya ci gaba da jagorantar al'umma.

Sai dai wasu daga cikin sarakuna musamman yan gidajen sarauta na ganin cewa dole ne a dauki matakin tsige Sarkin da maye gurbinsa, domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al'umma.

Matakin farko da Gwamna Adeleke ya dauka

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi umarni a sauke farashin abinci domin talaka ya samu sauki

Da yake magana kan lamarin a karon farko, Gwamna Adeleke ya bayyana hukuncin da aka yankewa Sarkin da abubuwan da suka biyo baya a matsayin abu mara dadi.

Kalaman gwamnan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kan Jama'a, Kolapo Alimi, ya fitar bayan zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar Osun da aka yi har zuwa daren Jumma’a.

Gwamnan Adeleke ya ce ya umurci Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu da ya dauki mataki cikin gaggawa kan wannan lamari.

“Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu ya dauki mataki kan ci gaba mara dadi da aka samu a Ipetumodu bayan garkame Sarki a Amurka,” in ji Adeleke.
Gwamna Adeleke da Sarkin Ipetumodu.
Hoton Gwamna Ademola Adeleke da na Sarkin Ipetumodu Hoto: Ademola Adeleke
Source: Facebook

Martanin sarakunan Ipetumodu

A gefe guda, gidan sarautar Aribile a bayyana umarnin gwamnan a matsayin mataki mai kyau, yana mai cewa al'umma suna jiran a yi abin da ya dace.

Yarima Ayoola Olaboye, wanda ya yi magana da Vanguard kan wannan batu, ya ce:

“Umarnin gwamnan ya dace da abin da al’ummarmu ke sa ran samu, kuma muna ganin wannan matakin yana kan hanya.”

Kara karanta wannan

Da gaske an kwace sarautar da Sarki ya ba Shugaba Tinubu a Arewa? Gaskiya ta fito

A bangarensa, shugaban masu zaben sarki, Cif Sunday Adedeji, ya bayyana cewa masu zaben sarki za su jira umarni kafin daukar mataki na gaba.

Ana fargabar zanga-zanga a Ipetumodu

A wani labarin, kun ji cewa an fara fargabar zanga-zanga na iya barkewa a yankin masarautar Ipetumodu kan abin da ya faru da Sarki a Amurka.

Rahotanni sun nuna cewa wasu mazauna garin sun fara shirye-shiryen gudanar da zanga-zanga don ganin an hanzarta zaben sabon sarki.

A halin yanzu, garin Ipetumodu na cikin wani yanayi na rashin tabbas, inda mutanen gari ke jiran makomar sarautarsu bayan daure Sarki a Amurka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262