Tsohon Soja Zai Bada Wuri, Simi Fubara Zai Koma Kujerar Gwamnan Rivers

Tsohon Soja Zai Bada Wuri, Simi Fubara Zai Koma Kujerar Gwamnan Rivers

  • Bayan watanni shida, an fara shirin dawo da jihar Rivers kan mulkin dimokuradiyya biyo bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara
  • Gwamnatin jihar Rivers ta sanar da tsare-tsaren da ta fara yi don dawowa kan turbar dimokuradiyya
  • Hakan na nufin aikin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shugaban riko, don jan ragamar jihar mai arzikin mai ya kusa zuwa karshe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers – Gwamnatin jihar Rivers ta fara shirye-shirye kan dawowa turbar mulkin dimokuradiyya.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa ta fara tsari na sauya mulkin da ake yi a bisa dokar ta baci zuwa dimokuradiyya.

Gwamna Fubara zai koma mulkin jihar Rivers
Hoton shugaban riko na jihar Rivers, Ibok-Ete Ibas da Gwamna Siminalayi Fubara Hoto: @SimFubaraKSC
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jiha, Farfesa Ibibia Lucky Worika, ya fitar a ranar Asabar, 13 ga watan Satumban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya sanya dokar ta baci a Rivers

Kara karanta wannan

Shanu sun cika Abuja: Fadar shugaban kasa, Sultan sun gana da Miyetti Allah

Idan ba a manta ba dai, a ranar Talata, 18 ga watan Maris 2025, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta baci a jihar Rivers.

Shugaban kasa ya kuma dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakinsa da 'yan majalisar dokokin jihar daga kan mukamansu.

Ya ce ya dauki matakin don dawo da oda a jihar mai arzikin man fetur da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.

Wane shiri aka fara kan mika mulki?

Gwamnatin ta sanar da cewa a cikin shirye-shiryen mika mulkin, za a gudanar da addu’ar godiya a coci ranar Lahadi, 14 ga watan Satumban 2025, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.

Za a gudanar da addu'ar godiyar ne a cocin Ecumenical Centre, da ke hanyar Abonima Wharf, a birnin Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.

An gayyaci manyan jami’an gwamnati, ciki har da manyan sakatarori, shugabannin kananan hukumomi, shugabannin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin kwamitoci da hukumomin jiha, da kuma shugabannin masana’antu.

Gwamna Fubara zai dawo kan mulki
Hoton gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara Hoto: @SimFubaraKSC
Source: Instagram

Shugaban riko a Rivers ya zama babban bako

An bayyana tsohon hafsan rundunar sojojin ruwa kuma shugaban riko na gwamnatin Rivers, Vice-Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin babban bako na musamman.

Kara karanta wannan

Majalisa ta kara wa gwamna karfi, ta sauya dokar nadawa da sauke Sarki daga mulki

Hakazalika, an umarci baki da su isa wurin tun karfe 9:30 na safe, yayin da za a fara addu’ar da misalin karfe 10:00 na safe.

"Gwamnatin jihar Rivers na farin cikin gayyatar manyan sakatarori, shugabannin kananan hukumomi, shugabannin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin hukumomi da ma'aikatu, shugabannin masana’antu, jami’an gwamnati da baki na musamman."
"Zuwa addu’ar godiya a matsayin wani bangare na bukukuwan shirn sauya mulki zuwa tsarin dimokuradiyya a jihar Rivers.”

- Farfesa Ibibia Lucky Worika

Wike ya magantu kan dawowar Fubara mulki

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan lokacin da Gwamna Siminalayi Fubara, zai dawo kan kujerarsa.

Nyesom Wike ya nuna cewa dakataccen gwamnan na jihar Rivers zai dawo kan kujerarsa a ranar 18 ga watan Satumban 2025.

Ministan na birnin Abuja ya yi wannan jawabin ne dai lokacin da yake ganawa da manema labarai kan zaben kananan hukumomin jihar da aka gudanar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng