Sojoji Sun Kashe Jagoran 'Yan Ta'adda, Kachalla Babangida bayan Gumurzu
- Sojojin Najeriya karkashin Operation Accord III sun yi nasarar kashe mataimakin shugaban ‘yan ta’adda a jihar Kogi
- Dakarun sun yi arangama da miyagun ne a cikin daji bayan samun sahihin bayanan sirri kan wajen da suke haduwa
- Bayan nasarar, rundunar ta ce za ta ci gaba da sintiri da kai farmaki don kawar da barazanar ‘yan ta’adda a fadin jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi – Sojojin Najeriya karkashin Operation Accord III sun ce sun yi nasara a wani samame da suka kai kan ‘yan ta’adda a jihar Kogi.
Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun samu gagarumar nasara, inda suka hallaka wani fitaccen mataimakin shugaban 'yan ta'adda.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa hakan ya biyo bayan rahoton sirri da sojojin suka samu kan wasu ‘yan ta’adda da ke shirin tsallaka dajin Ofere zuwa yankin Ayetoro Gbede.

Kara karanta wannan
An bankado abubuwa, matar shedanin 'dan bindiga ta shiga hannu a Zamfara, ta tsure
Rundunar ta ce wannan na daga cikin matakan da suke dauka don tabbatar da an kawar da ta’addanci da sauran miyagun laifuffuka a fadin jihar.
Yadda sojoji suka yi nasara a Kogi
Rahoton ya bayyana cewa dakarun sun kafa shingen kwanton bauna a kusa da hanyar da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda za su bi.
Duk da cewa ba su hadu da su a farko ba, daga baya bayan sun koma sansani sai 'yan ta'addan suka yi wa sojoji kwanton bauna.
Sai dai da karfin makamai da dabarun yaki, sojojin sun yi nasarar fatattakar miyagun tare da yi musu illa sosai.
Bayan haka suka binciki yankin, inda suka gano harsasai, wayoyin salula 31, kwayoyi, na’urar duba jini, kayan tsafi, da kuma kudi N16,000.

Source: Facebook
Sojoji sun kashe Kachalla Babangida
Daga cikin 'yan ta'addan da suka tsere da raunukan harbin bindiga akwai wanda ake kira Babangida Kachalla.
Babangida ne mataimakin shugaban wata kungiyar ‘yan ta’adda da ke aiki karkashin Kachala Shuaibu.
Bayan karin bayani daga sahihan hanyoyin sirri, an tabbatar da cewa Babangida Kachala ya mutu sakamakon harbin da ya samu a fafatawar.
Sojoji za su cigaba da aiki a Kogi
Sojojin Najeriya sun ce za su ci gaba da mamaye dajin Ofere da kewaye ta hanyar sintiri da kwanton bauna domin tabbatar da babu wata mafakar ‘yan ta’adda.
Rundunar ta kuma yi kira ga jama’ar Kogi da su ci gaba da bayar da bayanai na gaskiya don taimakawa sojojin wajen kai hari da fatattakar kungiyoyin miyagun.
A cewar rundunar, kwarin gwiwar sojoji na nan daram, kuma za su ci gaba da matsa lamba ga ‘yan ta’adda har sai sun kawar da su baki daya daga jihar.
Za a gurfanar da dan ta'adda Albarnawi
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar DSS ta shigar da kara kan shari'ar da aka fara yi wa shugaban 'yan ta'adda da ake kira da Al-Barnawi.
DSS ta koka kan yadda shari'ar dan ta'addan ke cigaba da tafiyar hawainiya bayan kama shi da aka yi a shekarun baya.

Kara karanta wannan
'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina
Rahotanni sun bayyana cewa Al-Barnawi ake zargi da kai hari ofishin majalisar dinkin duniya, inda ya jawo asarar rayuka.
Asali: Legit.ng
