Gwamna Ya Amince da Shawarar Majalisar Sarakuna, Ya Kara Nada Sarki Mai Daraja
- Gwamnan jihar Kuros Riba ya amince da nadin Orbon (Sir) Celestine Awor a matsayin sabon Sarkin kabilar Ekinta Clan
- Mai ba gwamnan shawara kan harkokin masarautu Francis Edet ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar
- Wannan nadi dai na zuwa ne bayan korafin da Majalisar Sarakuna suka kai wa mai girma gwamna kan bukatar nada sabon Sarki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Cross River - Gwamnan jihar Kuros, Bassey Otu, ya nada sabon Sarkin kabilar Ekinta da ke karamar hukumar Akamkpa.
Gwamna Otu ya nada basaraken ne bayan majalisar zaben Sarki a masarautar Ekinta Clan ta gudanar da zabe kuma sun mika masa sunan wanda ya dace.

Source: Twitter
Mai bai wa gwamnan jihar Kuros Riba shawara kan harkokin sarauta, Francis Edet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Otu ya nada Sarkin Akinta
Ya ce Gwamna Bassey Otu ya amince da nadin Mai Martaba, Orbon (Sir) Celestine Awor a matsayin sabon Sarkin kabilar Ekinta Clan a karamar hukumar Akamkpa ta jihar.
Mista Edet ya ce Sarkin shi ne wanda masu zaben suka gabatar wa gwamna bayan bin duka dokoki da ka'idojin da aka tanada.
A wata wasika mai dauke da kwanan wata 8 ga Satumba, 2025, sashen harkokin sarauta ya sanar da amincewar Gwamna Otu tare da tabbatar masa da sarauta.
Wasikar ta kuma gayyaci sabon Sarkin tare da Majalisar masarautarsa zuwa bikin tabbatar masa da kujerar sarauta, ta ce za a tsara bikin cikin kwanaki 30 masu zuwa.
Gwamna zai mika takardar nadi ga Sarki
Bayan wannan, gwamna zai mika masa takardar shaida ta amincewa da nada shi a matsayin Sarkin kabilar Ekinta na dindindin.
Wannan dai na zuwa ne bayan takardar korafin da Majalisar Sarakunan Ekonganaku ta mika wa Gwamna Otu a ranar 13 ga watan Janairu, 2025.
Sarakuna biyar ne suka sanya hannu a takardar korafin, wacce ta tunawa gwamnan batun Sarkin da aka soke nadinsa da bukatar lalubo sabon mai martaba.

Source: Facebook
Yadda aka bi doka wajen nada basaraken
Wani basarake da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Post cewa nada Awor a matsayin Sarki ya yi daidai da dokar jihar Kuros Riba mai lamba 1 ta shekarar 1996.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, sabon Sarkin gargajiya, Celestine Awor, ya yi alkawarin yin mulki da tawali’u, hikima da tsoron Allah.
Ya ce zai yi iya bakin kokarinsa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga mutanensa domin daga martabar kabilar zuwa matsayi mai daraja.
An nemi gwamna ya madin Sarki a Ogun
A wani labarin, kun ji cewa zaben Bashorun Oluwole Ogunbayo da Majalisar masu nada Sarki suka yi a jihar Ogun ya tayar da kura a masarautar Isara-Remo.
’Yan asalin Isara-Remo da ke ƙaramar hukumar Remo ta Arewa a jihar Ogun, sun koka kan tsarin da aka bi wajen zaɓen sabon Odemo na Isara-Remo.

Kara karanta wannan
Majalisa ta kara wa gwamna karfi, ta sauya dokar nadawa da sauke Sarki daga mulki
Jama'ar yankin masarautar sun yi zargin cewa masu alhakin zaben Sarki ba su bi hanyar da doka da al'adar gargajiya ta shimfida ba wajen zabo mai martaba, sun shigar da korafi gaban gwamna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

