Shirin da Gwamna Abba Kabir Ya Yi kan Auren Jinsi a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da tura kudiri zuwa majalisar dokokin Kano wanda yake magana kan auren jinsi
- Ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sassauci ba kan dab'iun da suka sabawa koyarwar al’ada da addinin Musulunci a jihar Kano
- Gwamna Abba ya ba da tabbacin cewa duk wadanda aka samu da laifi, za su dandani kudarsu yadda ya dace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da mika wani kudiri ga majalisar dokokin jihar kan auren jinsi.
Gwamna Abba ya amince da tura kudirin ne wanda ke neman haramta auren jinsi da wasu dabi’un da aka dauka a matsayin haram a jihar.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya shirya haramta auren jinsi
Gwamna Abba Yusuf ya bayar da amincewar ne a yayin zaman majalisar zartarwa ta jihar karo na 31 da aka gudanar a Kwankwasiyya City.
A cikin sanarwar, gwamnan ya ce gwamnatin Kano ba za ta yi sassauci ba wajen kare koyarwar addinin Musulunci da kuma al’adun jihar.
Ya jaddada cewa dole ne jihar ta ci gaba da kare kimarta ta fuskar al'ada da kuma addini.
Abubuwan da kudirin ya shafa
Gwamnan ya bayyana cewa kudirin ya haramta auren jinsi da kuma dabi’un da ake kira a nan gida da Madigo da Liwadi, wadanda gwamnati ta dauka a matsayin abubuwan da suka sabawa addini.
“Babu a irin yanayin da za mu bari ayyukan da suka sabawa addini da al’adu su samu tushe a Kano. Wannan gwamnati na da nauyin kare mutuncin tarbiyyar al’ummarmu."
"Idan aka amince da kudirin ya koma doka, duk wanda aka kama da aikatawa ko yada auren jinsi da makamantansa zai fuskanci hukunci mai tsauri."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Ana sa ran majalisar Kano za ta hanzarta
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kwarin gwiwar cewa majalisar dokokin jihar za ta yi abin da ya dace ga kudirin da gaggawa.
Ya nuna fatan majalisar za ta yi hakan ne saboda muhimmancin kudirin ga rayuwar al’umma da mutuncin jihar Kano.

Source: Twitter
Shin Najeriya ta haramta auren jinsi?
A shekarar 2013, 'yan majalisun Najeriya sun amince da kudirin da ke haramta auren jinsi, tare da yin tanadin daurin shekara 14 a gidan gyaran ga wadanda aka samu da laifin, gidan jaridar BBC ta kawo rahoton.
Hakazalika, a shekarar 2014, Shugaba Goodluck Jonathan ya rattaba hannu kan kudirin, wanda hakan ya mayar da shi doka.
Abin a yaba ne
Hassan Danbuba wanda yake zaune a Kano ya shaidawa Legit Hausa cewa mika kudirin dokar a abin a yaba ne.
"A matsayinmu na Musulmai muna maraba da.wannan doka. Domin wadannnan munanan dabi'un sun sabawa koyarwar addinin Musulunci"
- Hassan Danbuba
Kananan hukumomi za samu 'yanci a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da goyon baya ga sabuwar dokar da za ta ba da 'yanci ga kananan hukumomi.
Gwamna Abba ya ba da tabbacin cewa yana goyon bayan kananan hukumomin jihar su samu 'yanci, musamman ta fuskar juya kudadensu.
Hakan na zuwa ne bayan majalisar zartaswar jihar ta mika kudirin dokar ga majalisar dokokin Kano, don fara nazari a kansa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


