Karar Fashewar Abu Ta Tayar da Hankula a Madina, kusa da Masallacin Annabi SAW
- Rahotanni sun ce an ji karar fashewar abubuwa a sama kusa da Masallacin Annabi a safiyar 11 ga Satumba, 2025
- Biyo bayan aukuwar lamarin, hukumomin Saudiyya sun tabbatar faruwar shi kuma sun bukaci a daina yada jita jita
- Saudiyya ta roƙi jama’a da su guji hasashen abin da ya faru, su jira bayanai masu inganci daga hukumomin da abin ya shafa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudiyya – A safiyar ranar Alhamis 11 ga Satumba, 2025, bayan sallar Asubah, an ji karar fashewar abubuwa a sassan Madina, ciki har da yankin da ke kusa da Masallacin Annabi (SAW).
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa karar ta biyo bayan fashewar wasu abubuwa ne a sararin sama.

Source: Getty Images
Hukumomin kasar Saudiyya sun fitar da sanarwa ne a wani sako da shafin Inside the Haramain ya wallafa a X.

Kara karanta wannan
'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina
Martanin hukumomin Saudiyya
A wata sanarwa da aka fitar, hukumomin Saudiyya sun ce abin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:43 na safiya bayan sallar Asuba.
Sun bukaci jama’a da su guji yada jita-jita ko hasashe kan lamarin, su kuma jira cikakken bayani daga hukumomin da abin ya shafa idan an kammala bincike.
Ana sa ran cewa za a samu cikakken bayani daga kasar Saudiyya bayan kammala bincike domin hankalin jama'a ya kwanta.
Martanin jama’ar duniya da addu’o’i
Al’umma daga sassa daban-daban sun bayyana damuwarsu tare da yin addu’a don tsaron birnin Madina da sauran ƙasashen Musulmi.
Wani mai amfani da Facebook, Aliyu Ibrahim ya yi magana a karkashin rubutun shafin Saudiyya da cewa:
“Mun yi imani cewa Allah zai ci gaba da kare birnin Makkah da Madina.
"Annabi (SAW) yana kwance a ƙasa a Madina, kuma muna da yakinin Allah zai ci gaba da kare shi da birnin bayan wafatinsa. Allah Ya kare sauran ƙasashen musulmi.”
Shi ma Abbas Morno ya yi addu'a da cewa:
“Allah Ya kiyaye birnin Madina tare da masu ibada a cikinsa.
"Allah Mai jin ƙai Ya kawar da duk wani ƙalubale da mummunan shiri da ake yi wa yankin Saudiyya da ƙasashen musulmi gaba ɗaya.”

Source: UGC
Wani da ya shaida lamarin kai tsaye, Hassaan Ahmad, ya ce:
“Na gani da idona bayan sallar Asuba kamar wani makami ya bayyana a sama, amma ban san menene ba a hakika.”
Sai dai wani mai suna Zafar Iqbal ya yi gargadi cewa jinkirin hukumomi wajen fitar da bayanai na iya haifar da yaɗuwar jita-jita.
Iqbal ya ce:
“Idan hukumomi suka yi jinkiri, hasashe zai yawaita. Ya kamata su fito da bayanin da wuri.”
Saudi ta goyi bayan Gaza kan Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta nuna goyon bayanta ga Falasdinawa domin samun damar kafa kasarsu.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana cewa ya yi wayar tarho da Yariman Saudiyya kan goyon bayan Falasdinu.
Kasashen duniya na cigaba da goyon bayan kafa kasar Falasdinawa ne domin kawo karshen hare haren da Isra'ila ke kai musu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

