Gwamna Dauda Ya Samu Gargadi bayan Ma'aikatan Jinya Sun Shiga Yajin Aiki a Zamfara

Gwamna Dauda Ya Samu Gargadi bayan Ma'aikatan Jinya Sun Shiga Yajin Aiki a Zamfara

  • Ma'aikatan jinya a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani saboda wasu bukatu da su ke son gwamnati ta biya musu
  • Sun zargi ma’aikatar lafiya ta fifita likitoci tare da ware ma'aikatan jinya kan sabon tsarin albashi da aka bullo da shi
  • Ma'aikatan sun ba Gwamna Dauda Lawal sa’o’i 24 ya warware matsalar ko kuma fuskanci matsalolin da za su kawo cikas a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Gamayyar kungiyar ma'aikatan jinya a jihar Zamfara ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani.

Ma'aikatan jinyan sun shiga yajin aikin ne kan abin da su ka kira wariyar da aka nuna musu wajen sabon tsarin albashi da gwamnatin jihar ta amince da shi.

Ma'aikatan jinya sun shiga yajin aiki a Zamfara
Hoton gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da aka rubuta ranar, 11 ga watan Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu ta dauki mataki bayan ma'aikata sun yi zanga zanga a kanta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Kabiru Zamau ne ya sanya hannu kan wasikar a madadin kungiyar.

Meyasa ma'aikatan jinya shiga yajin aiki?

Kungiyar ta zargi ma’aikatar lafiya ta jihar da ware sama da ma'aikatan jinya 1,000 daga cikin wadanda za su amfana da sabon tsarin albashi.

Sabon tsarin dai an kawo shi ne don ma'aikatan lafiya, amma an aiwatar da shi ne kawai ga likitoci

Kungiyar ta ce dukkan kokarin da su ka yi wajen jawo hankalin gwamnati ya ci tura, don haka suka janye ayyukansu daga cibiyoyin kiwon lafiyar gwamnatin jiha.

“Idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba cikin sa’o’i 24 masu zuwa, ma'aikatan jinya a cibiyoyin lafiya na tarayya ciki har da asibitin FMC Gusau za su shiga yajin aikin tare da mu."

- Dr. Kabiru Zamau

Wane gargadi su ka yi wa gwamnan Zamfara?

Kungiyar ta yi gargadin cewa yajin aikin na iya tsananta matsalar cutar kwalara wadda aka samu barkewarta a jihar.

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki? Gwamnatin tarayya ta karyata shirin daukar sababbin ma'aikata

"Barin gaba daya ma'aikatan jinya sun janye ayyukansu a wannan lokaci mai muhimmanci, saboda rashin adalcin da wani jami'in gwamnati ya yi, zai zama gazawa ta fannin jagoranci."

Dr. Kabiru Zamau

Ma'aikatan jinya sun gargadi Gwamna Dauda Lawal
Hoton gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Dauda Lawal
Source: Twitter

Ma'aikata sun yi kira ga Gwamna Dauda

Kungiyar ta bukaci Gwamna Dauda Lawal ya sa baki kai tsaye ta hanyar umurtar ma’aikatar lafiya ta warware matsalar, da kuma tabbatar da shigar da ma'aikatan jinyan cikin sabon tsarin albashin tun daga watan Satumba.

Sun ce rashin yin hakan zai jefa tsarin kiwon lafiyar jihar cikin rikici, abin da zai yi barazana ga rayukan al’umma da cutar kwalara ta riga ta yi barazana a kansu

Yajin aiki ya haifar matsala

Wani mazaunin birnin Gusau a Zamfara, Jamilu Abdullahi, ya shaidawa Legit Hausa cewa yajin aikin ya kawo tsaiko a asibitoci.

Ya bayyana cewa marasa lafiya da dama sai dai aka dawo da su gida saboda babu masu kula da su.

"Ni nan kaina akwai kakarmu da ba ta da lafiya amma dole sai dai muka dawo da ita gida. Hakan ya kasance ga sauran mutane masu marasa lafiya."

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya kori malamin makaranta daga aiki bayan ya aikata babban laifi

- Jamilu Abdullahi

Likitoci sun fara yajin aiki a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki reshen birnin tarayya Abuja, (ARD-Abuja), ta shiga yajin aiki na gargadi.

Likitocin sun nuna bacin ransu kan yadda gwamnatin tarayya ke kin cika musu bukatunsu, wanda hakan ya sanya suka janye ayyukansu daga asibitocin birnin tarayya.

Shugaban kungiyar Dr. George Ebong ya bayyana cewa sun cimma matakin shiga yajin aikin ne bayan wani taron da su ka gudanar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng