'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kan Matafiya a Sokoto, an Yi Barna

'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kan Matafiya a Sokoto, an Yi Barna

  • ’Yan bindiga dauke da makamai sun tare hanya a jihar Sokoto, inda su ka bude wuta kan motocin da ke dauke da fasinjoji
  • Motocin na haya suna dauke da fasinjoji ne wadanda su ka dawo daga kasuwa neman na abinci
  • Dakarun sojojin Najeriya sun kai daukin gaggawa bayan samun rahoton tarkon da 'yan bindigan su ka dana

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - 'Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki kan motocin haya da su ke dauke da fasinjoji a jihar Sokoto.

Harin da 'yan bindigan dauke da bindigogin AK-47 suka kai a karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto, ya yi sanadiyyar raunata fasinjoji guda bakwai.

'Yan bindiga sun harbi fasinjoji a Sokoto
Hoton gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu da shugaban 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: @Ahmedaliyuskt, @PoliceNG
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun bude wuta a Sokoto

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu nasara kan 'yan bindigan da su ka shirya ta'asa a Katsina

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na dare a ranar Laraba, 10 ga Satumban 2025.

'Yan bindigan sun tare hanyar ne da ke tsakanin kauyukan Kogoho Lambar Tofa da Kogogo Rijiya a karamar hukumar Rabah.

Majiyoyin sun bayyana cewa ’yan bindigan sun bude wuta ne kan motoci uku wadanda ke dauke da fasinjoji, wadanda suka fito daga kasuwar Achida suna kan hanyarsu ta zuwa garin Rabah.

Harin 'yan bindiga ya jawo fasinjoji sun jikkata

Duk da cewa direbobin motocin sun ki tsayawa, inda su ka samu su ka tsere, fasinjoji bakwai sun samu raunuka daban-daban.

"Direbobin sun ki tsayawa inda su ka samu su ka tsira daga harin, amma fasinjojinsu guda bakwai sun samu raunuka daban-daban."

- Wata majiya

Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma sun yi gaggawar zuwa wurin, bayan samun rahoton lamarin.

Sojojin sun yi artabu da 'yan bindigan har suka tilasta musu ja da baya tare da yiwuwar samun raunukan harbin bindiga.

An tura wadanda suka jikkata asibiti

An garzaya da fasinjojin da su ka jikkata zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Usmanu Danfodiyo (UDUTH) domin samun kulawar likitoci.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga, an samu asarar rayuka

Majiyoyin na tsaro sun kara da cewa an kara tsaurara sintiri a kan hanyar domin hana sake faruwar irin wannan hari.

'Yan bindiga sun farmaki matafiya a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

Sojoji sun fafata da 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun fafata da 'yan bindigan ne bayan sun yi musu kwanton bauna, lokacin da su ke rakiyar 'yan kasuwa a karamar hukumar Gusau.

Musayar wutar da aka yi a tsakanin bangarorin biyu, ta yi sanadiyyar rasa rayukan sojoji guda biyar, yayin da aka hallaka 'yan bindiga masu tarin yawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng