Birtaniya Ta Dage Takunkumin Tafiye Tafiye da Ta Kakaba wa Jihar Kaduna
- Gwamnatin Birtaniya ta cire Kaduna daga jerin wuraren da aka hana tafiya saboda matsalolin tsaro da tashe-tashen hankula
- Wannan na zuwa ne bayan ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kara hadin gwiwa a fannonin lafiya, ilimi da noma da jihar
- A bayaninsa, Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan a matsayin tabbaci kan nasarorin da aka samu a tsaro da cigaban al'umma
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa ta cire jihar Kaduna daga jerin wuraren da ta hana 'yan kasarta zuwa, wato jerin “Red list”, ta mayar da jihar cikin jerin “Amber”.
Wannan mataki na nufin cewa, ana iya tafiya Kaduna ba tare da wata gagarumar matsala ba kamar yadda ake yi a baya.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa an ruwaito cewa wannan sauyin ya biyo bayan ingantuwar tsaro da cigaban da aka samu a jihar karkashin mulkin Gwamna Uba Sani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Birtaniya ta cire takunkumin tafiya zuwa Kaduna
Vanguard ta ruwaito cewa janye takunkumin na kunshe a cikin sanarwar ta fito ne yayin da gwamnatin jihar Kaduna ta rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da ofishin UK.

Source: Facebook
Wannan yarjejeniya na nufin kara hadin gwiwa tsakanin Kaduna da Birtaniya a fannonin mulki, ilimi, kiwon lafiya, noma da sauye-sauyen tsari.
Cynthia Rowe, Daraktar Ci gaba ta Burtaniya a Najeriya, ta ce:
“Wannan mataki yana nuna amincewa da ci gaban da Kaduna ta samu a tsaro da sauye-sauyen gwamnati. Yanzu, kofar jihar Kaduna a bude ta ke ga masu zuba jari da kungiyoyin ci gaba.”
Gwamnan Kaduna ya bayyana jin dadinsa
Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan ci gaba a matsayin wani karin karfi ga manufofinsa na sauyi da cigaban jama’a.
Ya ce gwamnatin sa ta riga ta zuba 10% na kasafin kudin 2025 don bunkasa noman zamani da kiwon dabbobi, tare da inganta kiwon lafiya da ilimi.
Ya ce:
“Mun rage mace-macen mata da jarirai, mun bunkasa asibitoci da ajujuwa.”
Gwamnan ya kara da cewa ana aiwatar da shirye-shirye irin da dama don karfafa shiga al’umma a harkokin mulki.
Cynthia Rowe ta tabbatar da cewa Birtaniya za ta ci gaba da tallafa wa Kaduna, inda ta ce ba wai sanya hannu kadai ake yi ba, sai dai aiwatar da aiki na hakika da zai kawo cigaba ga al’umma.
Wannan mataki na cire Kaduna daga jerin wuraren da aka hana tafiye-tafiye na da matukar tasiri ga bunkasar zuba jari da ayyukan ci gaba.
An samu sauƙin hari a Kaduna
Hafsat Iliyasu Dambo, ƴar jarida ce da ke zaune a jihar Kaduna, ta kuma shaida wa Legit cewa an samu raguwar rahoton hare-hare a jihar.
Ta ce:
"A da, kusan kullum za ka ji labarin an kai hari wani wuri ko an kashe wasu. Amma yanJ gaskiya da sauƙi, ana kwana biyu ba a ji an kai hari ba."
'Yan ta'adda sun saki Kansila a Kaduna
A baya, mun ruwaito cewa Kansilan mazabar Gwantu a karamar hukumar Sanga, jihar Kaduna, David Ali, ya samu kubuta daga hannun ’yan bindiga bayan kwana huɗu.
An kai farmakin ne da 12:00 na dare a ranar Alhamis da ta gabata, inda wasu 'yan bindiga guda biyar suka kutsa cikin gidansa inda su ka yi awon gaba da shi iyalansa na kallo.
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce an sako David Ali ne a dajin da ke kusa da Ninzo, bayan biyan fansa da iyalansa su ka yi har na N4,000,000.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


