Asiri Ya Tonu: Gwamnati Ta Bankado Ma'aikatan Bogi a Bauchi, Za Su Fuskanci Hukunci
- Hukumar da ke da alhakin kula da asibitocin jihar Bauchi ta gano ma’aikatan bogi sama da 100 a bangaren lafiya
- An shirya mika sunayensu ga Gwamna Bala Mohammed domin daukar mataki bisa ka’idar aikin gwamnati
- An dai zakulo ma'aikatan ne bayan hukumar kula da asibitocin ta dukufa wajen gudanar da aikin tantancewa sakamakon korafe-korafen da ake yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi – Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da cewa ta gano sama da ma’aikatan bogi 100 a bangaren lafiya.
Gwamnatin ta sha alwashin hukunta su bisa dokokin aiki da aka amince da su.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa, shugaban hukumar kula da asibitocin jihar, Malam Sambo Alkali, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Bauchi ranar Alhamis, 11 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka zakulo ma'aikatan bogi a Bauchi

Kara karanta wannan
'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina
Shugaban hukumar ya ce an kammala bincike a wasu cibiyoyi guda biyar, wanda ya tona asirin ma’aikatan bogin, kuma za a mika sunayensu ga Gwamna Bala Mohammed domin daukar mataki.
"A yanzu haka muna aiki kan tantancewa domin zakulo ma'aikatan bogin da mutane su ke ta magana a kai."
"A baya-bayan nan, mun yi hakan a cibiyoyi biyar, inda muka samu fiye da ma'aikatan bogi guda 100, wadanda za mu mika sunayensu ga gwamna."
- Malam Sambo Alkali
Malam Sambo Alkali ya ce matsalar karancin likitoci ya zama babban kalubale a duniya baki daya, amma a Bauchi, Gwamna Bala ya amince da wani shiri da ya fara kawo sakamako mai kyau.
Ya bayyana cewa an dauki sama da likitoci 40, ciki har da masu ba da shawara, a karkashin shirin, kuma an rarraba su bisa tsarin bincike da bayanan da aka tattara, rahoton Premium Times ya tabbatar da labarin.
"Shirin ya tanadi likitoci masu kulawa da asibitoci, kuma suna da alhakin dubawa da kula da yadda cibiyoyin lafiya ke tafiya."
- Malam Sambo Alkali
Likitocin Bauchi za su samun karin albashi
Malam Sambo Alkali ya kara da cewa Gwamna Bala ya umurci kwamitin lafiya na jihar da ya kirkiro tsarin albashi na musamman, domin jawo kwararru su zo su yi aiki a Bauchi.
A cewarsa, shirin ya kunshi daidaita albashin ma’aikatan lafiya na jihar da na gwamnatin tarayya domin kara musu kwarin gwiwa da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.

Source: Facebook
Karanta wasu karin labaran kan Bauchi
- Albarkacin Shettima, an ƴanta fursunoni 59, an ɗauki nauyin karatun marayu a Bauchi
- Bauchi: Hukumar BASIEC ta sanya ranar gudanar da zaben kananan hukumomi
- Matasa sama da 100,000 za su amfana a sabon shirin da aka kaddamar a Bauchi
Gwamna Bala zai gyara titi kan biliyoyi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed, ta shirya yin aikin gyaran titi a karamar hukumar Misau.
Gwamnatin ta amince da kashe makudan kudaden da su ka kai Naira biliyan 6.5 don aikin fadada titin Misau wanda yake da tsawon kilomita 7.5.
Kamfanin da aka ba kwangilar aikin fadada titin na Misau, Mothercat, ya bayyana cewa za a kammala komai kafin karshen shekarar 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
