Okorodudu: Babban 'Dan APC Ya Rasu, Tinubu Ya Nuna Matukar Damuwa
- Shugaba Bola Tinubu ya yi jimamin rasuwar tsohon hafsan sojojin sama kuma jigon APC a Delta, Terry Okorodudu
- Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, gwamnatin jihar Delta da dukkan 'yan jam’iyyar APC baki ɗaya a Najeriya
- Tinubu ya yaba da gudummawar da marigayi Terry Okorodudu a bangaren siyasa da aikin soja a lokacin rayuwarsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alhini kan rasuwar tsohon hafsan sojin sama kuma jigon jam’iyyar APC a Jihar Delta, Terry Okorodudu.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun bayyana cewa Terry Okorodudu ya rasu yana da shekara 70 a duniya.

Source: Facebook
Fadar shugaban kasa ta wallafa a X cewa Tinubu ya ce rasuwar Okorodudu babban rashi ne ga jam’iyyar APC, jihar Delta da kuma ƙasa baki ɗaya.
Shugaban ya yi ta’aziyya ga matarsa, ‘ya’yansa, iyalansa da abokansa, tare da yi musu addu’ar Allah ya ba su haƙuri da juriya.
Gudummawar Marigayi Okorodudu ga Tinubu
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa Okorodudu ya taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka jam’iyyar APC a matakin jiha da ƙasa.
Ya tuna da yadda marigayin ya kasance cikin kwamitin tsaro na yaƙin neman zaɓensa a 2023, inda ya ba da cikakkiyar gudummawa wajen samun nasarar jam’iyyar.
Ya ce wannan aiki da tsantsar jajircewarsa sun tabbatar da kishin ƙasa da amincinsa ga al’ummarsa da jam’iyyar APC.

Source: Facebook
Aikin marigayi Okorodudu a gidan soja
Terry Okorodudu ya fara aikin soja a ranar 5 ga Janairu, 1976, lokacin da aka ba shi matsayin matukin jirgin sama a rundunar sojin saman Najeriya.
Ya yi aiki a rundunar na tsawon shekaru kafin ya yi ritaya, tare da bayar da horo ga daruruwan matasa jami’an soja.
Shugaba Tinubu ya bayyana shi a matsayin ɗan kishin ƙasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tsaron Najeriya.
Mukaman da marigayin ya riƙe
Tashar NTA ta wallafa a X cewa baya ga aikin soja, Okorodudu ya yi aiki a matsayin mai ba da tsaro a ofishin jakadancin Najeriya da ke Moscow, Rasha daga Fabrairu 2006 zuwa Yuli 2009.
Haka kuma, shi ne shugaban farko na kamfanin AETS wani reshe na rundunar sojin sama da aka kafa domin ƙarfafa harkar fasaha.
Ya kasance shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar Harry’s Friends Club, wadda ke bayar da shawarwari kan kyakkyawan mulki da inganta manufofin ci gaban kasa.
Dangantakar Okorodudu da shugaba Tinubu
Sanarwar ta kuma bayyana cewa marigayin ya kasance abokin siyasa na dogon lokaci ga Shugaba Tinubu, kuma ya nuna jajircewa wajen ba da goyon baya a fannoni da dama.
Shugaban ƙasa ya ce marigayin ya tsaya tsayin daka wajen kare mutuncinsa da neman ci gaban Najeriya, inda ya yi aiki cikin gaskiya da sadaukarwa.
Tinubu zai sauke farashin abinci
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya na cigaba da kokarin ganin farashin abinci ya sauka a Najeriya.
Karamin ministan noma na tarayyar Najeriya ne ya bayyana haka a wani taro da jami'an gwamnati suka yi a Abuja.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa gwamnatin za ta karya farashin ne bayan umarnin shugaba Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


