Gwamna Ya Yunkuro, Ya Bugi Kirji kan Samar da Hasken Wutar Lantarki na Awanni 24
- Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya tabbatar da cewa jihar za ta samu wutar lantarki na awa 24 a rana ta hanyar hadin gwiwa
- Ya tabbatar da cewa sun rattaba hannu kan yarjejeniya da hukumar samar da wuta a karkara domin kawo haske ga yankunan
- Gwamna Eno ya kara da bayyana cewa akwai shiri na musamman da gwamnatinsa ke yi a kan hasken lantarki a nan gaba kadan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Akwa Ibom– Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno ya bayyana cewa shirin gwamnatinsa ta tabbatar da wadatar hasken wutar lantarki a jihar.
Ya bayyan cewa gwamnatinsa da hukumar samar da wutar lantarki a karkara (REA) za su yi aiki tare domin tabbatar da samar da wutar lantarki na awa 24 a rana ga al’ummar jihar.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa gwamnan ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) da REA ne a yayin wani taron tattaunawa kan samar da wuta da aka gudanar a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Akwa Ibom ta kulla yarjejeniya da REA
Ibom Sons and Daughters ta wallafa a shafin Facebook cewa gwamna Eno ya ce wannan yunkuri na samar da wuta zai taimaka wajen inganta rayuwar mutane.
Ya ce shirin ya zama dole duba da yadda miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da rashin ingantaccen wuta duk da arzikin makamashi da ƙasar ke da shi.
Da yake zantawa da manema labarai a filin jirgin sama na Victor Attah International Airport bayan dawowarsa daga kasar Birtaniya, Gwamna Eno ya ce jiharsa ta shirya wani taro.
Ya bayyana cewa jihar za ta gudanar da taron samar da wuta a ranar 18 zuwa 19 ga Satumba, 2025, tare da haɗin gwiwa da REA.

Kara karanta wannan
Hukumar kwastam: Mutane kusan 600,000 sun nemi guraben aiki da ba su kai 4,000 ba

Source: Facebook
Ya ce:
“Muna bukatar mu bai wa al’ummar Akwa Ibom haske na awa 24 a rana. Wannan taro da ke tafe shi ne matakin gaba na aiwatar da hakan."
Gwamnan Akwa Ibom ya fadi dalilin zuwa Birtaniya
Ya kara da cewa yayin ziyararsa a Birtaniya, ya gana da Zakaran dambe Moses Itauma da kuma Gwamnan Islington, Utiofon Jackson, wadanda dukkanninsu 'yan asalin jihar Akwa Ibom ne.
Gwamnan ya ce irin nasarorin da suka samu a ƙetare abin alfahari ne, yana mai cewa:
“Wannan shi ne karo na biyu da muke da Gwamna daga Akwa Ibom, bayan Ukeme Awakessien-Jeter na Upper Arlington, Ohio a Amurka.”
Ya shawarci matasan jihar da su rungumi jajircewa da sadaukarwa, ba wai dogaro da gata ko jiran taimako daga wani ba.
Gwamnan ya nanata cewa shirin samar da wutar za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa masana'antu, samar da ayyukan yi, da kuma rage dogaro da inji a jihar.
Turakun wutar lantarki sun zube
A wani labarin, kun ji cewa Najeriya ta sake fuskantar babban koma‑baya a bangaren samar da wutar lantarki bayan da tushen wutar lantarki na ƙasa ya lalace a ranar Laraba.
Lamarin ya faru da 11:23 na safiyar Laraba, 10 ga Satumba, 2025, lamarin da ya yi sanadin katsewar wuta a jihohi da dama tare da kara ta'azzara matsalar rashin wuta.
Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC) ya fito da sanarwa inda ya ce rashin wutar ya samo asali ne daga lalacewar tushen wutar na ƙasa, wanda ya sa wutar da ake turo wa ta ragu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

