Ma'aikata Sun Yi Zanga Zanga, an Yi Zarge Zarge kan Ministar Tinubu

Ma'aikata Sun Yi Zanga Zanga, an Yi Zarge Zarge kan Ministar Tinubu

  • Ma’aikatan ma’aikatar harkokin mata sun yi zanga-zanga a birnin tarayya Abuja kan kin kula da walwalarsu
  • Sun koka game da rashin kayan aiki, biyan hakkoki da kuma takaita damar rubuta jarrabawar karin girma
  • Sun zargi ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, da yin watsi da bukatunsu na cikin gida

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ma’aikatan ma’aikatar harkokin mata ta tarayya sun gudanar da zanga-zanga a birnin tarayya Abuja.

Ma'aikatan sun gudanar da zanga-zangar ne kan abin da suka bayyana a matsayin kin kula da walwalarsu da ma’aikatar ke yi.

Ma'aikata sun yi zanga-zanga a ma'aikatar mata
Hoton ma'aikatan ma'aikatar mata na zanga-zanga da Minista Imaan Sulaiman-Ibrahim Hoto: @hm_womenaffairs
Source: Twitter

Ma'aikata sun yi zanga-zanga a Abuja

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ma'aikatan na ma'aikatar harkokin matan sun gudanar da zanga-zangar ne a ranar Laraba, 10 ga watan Satumban 2025.

A cikin wani bidiyo da ya yadu, masu zanga-zangar sun ce ma’aikatar ta gaza samar musu da kayan aiki, horo da kuma maido masu da kudin tafiye-tafiyen da suka kashe.

Kara karanta wannan

An dura kan Bashir Ahmad game da sukar kiran zanga zanga a Najeriya kamar Nepal

Wani ma’aikaci ya koka cewa har yanzu ba a biya su alawus na tafiye-tafiyen da suka yi tun watan Janairu da gaba daya na shekarar 2023 ba.

An yi zarge-zarge kan ministar mata

Wasu ma’aikata da suka yi magana ba tare da bayyana sunansu ba, sun ce tun lokacin da ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta hau kujerar, sai aka yi watsi da jin dadinsu.

“Babu kayan aiki, babu walwala. Ma’aikatan da suka cancanci rubuta jarrabawar karin girma ba a bari sun rubuta ba."

- Wani ma'aikaci

Wani ma'aikacin kuma ya ce ministar ta fi mayar da hankali ga shirye-shiryen waje na karfafa mata da matasa, amma ta yi watsi da bukatun cikin gida, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da labarin.

"Manufofin cikin gida sun fi muhimmanci a kan na waje. Kafin a karfafa wadanda ke waje, dole a karfafa wadanda ke aiki karkashinka."

- Wani ma'aikaci

Minista ba ta ce komai ba kan lamarin

Har yanzu Imaan Sulaiman-Ibrahim, wadda ta gaji Uju Kennedy-Ohanenye, bata mayar da martani kan zarge-zargen da ma'aikatan suke yi ba.

Kara karanta wannan

Tinubu: Sai da rajistar haraji za a yi hulda da banki a Najeriya daga 2026

Ma'aikata sun yi zarge-zarge kan ministar mata
Hoton Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim Hoto: @hm_womenaffairs
Source: Twitter

Zanga-zangar ta ma’aikatar harkokin mata na zuwa ne bayan irin hakan ya faru a wasu ma’aikatun gwamnati, ciki har da ta kudi.

Mambobin kungiyar TUC da tsofaffin ma’aikata sun gudanar da ta su zanga-zangar daban-daban a ma'aikatar kudi tun farkon wannan shekara.

Haka zalika, ma’aikatan ilimi da kiwon lafiya sun gudanar da yajin aiki kan batun biyan hakkokinsu na alawus.

Tsohuwar ministar mata ta magantu kan korarta

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohuwar ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta yi magana kan korar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi mata.

Uju Kennedy-Ohanenye ta bayyana cewa ko kadan ba ta yi nadama ba kan ayyukan da ta gudanar lokacin da take rike da mukamin.

Tsohuwar ministar ta bada tabbacin cewa duk da Shugaba Tinubu ya kore ta, za ta ci gaba da kare muradun gwamnatinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng