Tawagar Kasar Rasha Ta Dura Najeriya, ta Sauka a Jihar Neja
- Gwamna Mohammed Umaru Bago ya karɓi tawagar ‘yan kasuwa daga Rasha a Minna, babban birnin Jihar Neja
- Ziyarar ta biyo bayan yarjejeniyar da aka sanya hannu tsakanin gwamnatin jihar da bankin Sber na Rasha a wasu fannoni
- Tawagar ta yaba da yalwar filaye da albarkatun ruwa da jihar ke da su, tare da jaddada kudirin zurfafa haɗin gwiwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja – Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya tarbi wata tawaga ta ‘yan kasuwa daga Rasha a fadar gwamnatin jihar da ke Minna.
Ziyarar ta zo ne a matsayin cigaba na yarjejeniyar fahimtar juna da aka sanya hannu a baya tsakanin gwamnatin jihar da bankin Sber na Rasha.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan abubuwan da aka tattauna ne a cikin wani sako da mai magana da yawun gwamnan, Balogi Ibrahim ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhimmancin zuwan Rasha jihar Neja
A cewar gwamnan, hadin gwiwar za ta buɗe sababbin damammaki ga jihar musamman a bangaren noma da hakar ma’adinai.
Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da tabbatar da duk wani mataki da zai kai ga nasarar yarjejeniyar, ciki har da shirye-shiryen kiwon lafiya daga nesa (telemedicine) da ilimi.
Ya kara da cewa ziyarar ta zama alamar kyakkyawar makoma ga jihar Neja, inda ya gode wa tawagar da ta fito daga Rasha bisa wannan mataki na kulla haɗin kai.
Abin da 'yan Rasha suka gani a Neja
Shugaban kamfanin Niger Foods, Sammy Adigun, ya bayyana cewa tawagar ta zagaya gonaki da dama a jihar inda suka shaida yalwar filaye da kuma albarkatun ruwa da ake da su.
Peter Arseniev da sauran wakilan tawagar sun bayyana jihar Neja a matsayin abin burgewa da ban sha’awa, tare da nuna gamsuwa kan damar da jihar ke da ita wajen samar da abinci.
Sun gode wa gwamna Bago da kamfanin Niger Foods bisa ba su wannan damar na ganin irin dimbin albarkatun da ake da su a Neja a zahiri.

Source: Facebook
Alakar da Neja za ta kulla da Rasha
‘Yan kasuwar sun tabbatar da cewa suna da shirin ci gaba da zurfafa haɗin kai tare da buɗe sababbin hanyoyi da za su taimaka wajen amfani da albarkatun jihar yadda ya kamata.
Tawagar ta ce hakan ya nuna irin kudurin da Rasha ke da shi wajen yin aiki tare da Jihar Neja a fannin noma da sauran bangarori da za su inganta tattalin arzikin kasa baki ɗaya.
A daren ziyarar, gwamnatin jihar ta shirya liyafar girmamawa ga tawagar, inda aka karrama su da abinci iri-iri da kuma nishadantar da su da raye-raye da wakokin gargajiya.
Tawagar ta ƙunshi wakilai daga bankin Sber, hukumar cinikayyar Rasha, abokan hulɗa na kamfanin Rostselmash, karkashin jagorancin Peter Arseniev.
Bago ya gayyaci 'yan bola jari a Neja
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya koka kan yawan sace-sace da sunan bola jari a Neja.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya zauna da wasu daga cikin shugabannin 'yan bola jari domin samar da mafita.
Biyo bayan zaman da suka yi, Umaru Bago ya shirya wani zama na musamman da shugabannin bola jari na dukkan kananan hukumomin jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


