‘Sau 2 ba Mu Sallar Juma’a’: Musulmai Sun Roki Sauya Ranar Nadin Sarki da Za a Yi
- Kungiyar MURIC ta yi Allah wadai kan sanya ranar nadin Sarki da za a yi a karshen watan Satumbar wannan shekara ta 2025
- MURIC ta bukaci dage bikin mika sandar sarautar Sarkin Ibadan da aka shirya ranar Juma’a, saboda zai hana Musulmi gudanar da Sallah
- Farfesa Ishaq Akintola ya tuna matsalolin da Musulmi suka sha samu a baya kan wannan matsala da ta taba tasowa a baya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Kungiyar Kare Hakkokin Musulmi ta Kasa (MURIC) ta yi kira da a dage bikin miƙa sandar sarauta da aka shirya a ranar Juma'a.
Kungiyar ta bayyana damuwa kan yawan matsaloli da Musulmi suka samu a baya game da irin wannan biki da aka yi.

Source: Facebook
Rahoton Aminiya ya ce shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola shi ya bukaci daga ranar bikin domin mutunta mabiya addinin Musulunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe za a gudanar bikin nadin Sarkin Ibadan?
Hakan ya biyo bayan shirin nada sabon Sarkin Ibadan da aka fi sani da Olubadan da aka shirya ranar Juma’a wanda ya jawo suka musamman saboda muhimmancin ranar.
Hukumomi sun shirya gudanar da bikin ne a ranar 26 ga watan Satumar 2025 da muke ciki bayan mutuwar marigayi tsohon Sarki.
Rahotanni daga jihar Oyo sun nuna cewa Gwamna Seyi Makinde ya amince da nadin sabon Sarkin a matsayin Olubadan na 44.
Tsohon gwamna zai dare kujerar sarauta
Wannan dai na zuwa ne bayan rasuwar tsohon Sarkin Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, a jihar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
Majalisar masu nada Sarki na Olubadan ta zabi tsohon gwamna Rashidi Ladoja a matsayin wanda zai maye gurbin marigayi.
Masu nadin sarautar sun dauki matakin saka sunan Ladoja ne a Ibadan duk da cewa bai halarci taron da aka gudanar ba.

Source: Twitter
Nadin sarauta: MURIC ta dauki zafi a Oyo
Sai dai kungiyar MURIC ta yi Allah wadai da sanya ranar Juma'a wanda ya yi daidai da lokacin da Musulmai ke gudanar da addu'o'insu.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce:
"Sau biyu irin wannan matsala ta faru a baya, inda Musulmi suka kasa gudanar da Sallar Juma’a."
Wane zargi MURIC ke yiwa Gwamna Makinde?
MURIC ta kuma soki Gwamna Seyi Makinde da kokarin mayar da ranar Juma'a a matsayin ranar da ya ware domin yin wasu bukukuwa.
Akintola ya kara da cewa:
"MURIC ba za ta amince da yunƙurin mayar da Juma’a ranar bukukuwan Kiristoci ba."
Saboda haka ya bukaci a mayar da Juma’a ranar addu’o’in Musulmi domin girmama sabon Sarkin Ibadan, ko kuma a dage bikin zuwa Asabar.
MURIC ta zargi jami'a da tilasta Musulmai zuwa coci
Kun ji cewa Kungiyar MURIC ta zargi jami’ar Adeleke da hana dalibai Musulmi gudanar da ibadun Ramadan, ana tilasta musu halartar coci.

Kara karanta wannan
Da gaske an kwace sarautar da Sarki ya ba Shugaba Tinubu a Arewa? Gaskiya ta fito
MURIC ta ce jami’ar ta katse sallar tarawihi da dalibai suka gudanar, tare da gargaɗinsu da kada su sake yin hakan a harabar makarantar.
Kungiyar ta bukaci NUC da ta binciki dokokin jami’ar, tana mai cewa an haramta sallah da sanya hijabi, kuma ana tauye ‘yanci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

