Tinubu da Kansa Ya Fadi Abubuwan da Ya Tattauna da Shugaban Kasar Faransa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ganawarsa da shugaban Faransa Emmanuel Macron ta kasance mai amfani da fatan ƙarfafa haɗin kai
- Ya bayyana cewa tattaunawar ta shafi muhimman fannoni na haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Faransa don samun bunƙasar tattali da zaman lafiya
- Legit.ng Hausa ta gano cewa Bola Tinubu ya fara hutu na kwanaki 10 a Faransa da Birtaniya bayan dawowa daga ziyarar aiki a Japan da Brazil
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
France – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana bayan ganawarsa da shugaban Faransa, Emmanuel Macron.
Tinubu ya bayyana cewa sun yi tattaunawa mai amfani da ke da nufin ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Faransa.

Source: Facebook
Shugaban ya bayyana hakan ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba jim kadan bayan sun tattauna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da Tinubu ya tattauna da Macron
A cewar shugaba Tinubu, ganawarsu ta mayar da hankali ne kan kara hada kan Najeriya da Faransa domin cin moriyar juna.
Bayan ganawar, an jaddada muhimmancin ƙasashen biyu wajen yin aiki tare don kare muradun tattalin arziki da siyasa a matakin duniya.
Shugaban ya ce ya yi liyafa da Macron inda suka amince da sababbin matakai da za su inganta alaƙa tsakanin kasashen biyu.
Macron bai fitar da jawabi ba
Legit Hausa ta gano cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Emmanuel Macron ne a fadar Élysée da ke birnin Paris na kasar Faransa.
Awanni bauan Tinubu ya yi magana game da haduwar, mun bibiyi shafukan shugaban Faransa a dandalin X, amma ba mu samu komai ba.
Emmanuel Macron ya yi fitar da sanarwa game da wayarsa da Donald Trump da Sarkin Qatar, amma babu bayani kan zamansa da Bola Tinubu.
Hutun kwana 10 da Tinubu ya tafi
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Tinubu ya fara hutun kwana 10 tun daga ranar 4 ga Satumban 2025 inda zai huta tsakanin Faransa da Birtaniya kafin ya dawo Najeriya.
Rahoton tashar Channel TV ya nuna cewa hutun na zuwa ne bayan shugaban ya shafe mako biyu a ziyarar aiki a Japan da Brazil.
Hutun ya biyo bayan jerin ayyuka masu nauyi da ya gudanar a ziyarorinsa na baya-bayan nan, inda aka ce zai yi amfani da wannan lokaci wajen hutawa da kuma shirya tsare-tsare na gaba.

Source: Twitter
Tinubu ya je Faransa sau 2 a 2025
Wannan ziyara ce ta biyu da Tinubu ya kai Faransa cikin wata shida, bayan wata gajeriyar ziyarar aiki da ya gudanar a kasar a watan Afrilu, 2025.
A cewar fadar shugaban kasa, wannan na daga cikin matakan da Tinubu ke ɗauka na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da ƙasashen duniya.
Haka zalika gwamnatin tarayya ta ce ziyarar shugaban kasan za ta taimaka wajen jawo masu zuba jari don bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.
Tinubu zai karya farashin abinci
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi umarni da a sake karya farashin kayan abinci a fadin Najeriya.
Karamin ministan noma na kasa ne ya bayyana haka a wani taron da aka gudanar a birnin tarayya Abuja ranar Laraba, 8 ga Satumba, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa umarnin shugaban kasar ya kunshi samar da hanyoyin jigilar abinci daga gona zuwa kasuwanni cikin sauki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

