Akwai Kura: Malami Ya Yi Hasashe Shugabannin Kasashen da Za a Iya Sacewa a Afrika
- Fasto Babatunde Elijah Ayodele ya yi gargadi ga shugabanni a Afrika bayan ya yi hasashen wani abu da zai iya faruwa da su
- Ya shawarci shugabannin kasashen Côte d’Ivoire da Kamaru kan su kara tsaurara matakan tsaro
- Malamin addinin ya kuma ce shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron, na da wani shirin boye kan kasashen Afrika da dama
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya yi gargadi ga shugabannin Afrika.
Primate Ayodele ya bayyana cewa wasu 'dakaru na musamman' na iya yin garkuwa da shugaban wata kasa a nahiyar Afrika.

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa malamin addinin kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane hasashe aka yi kan shugabannin Afrika?

Kara karanta wannan
Da gaske an kwace sarautar da Sarki ya ba Shugaba Tinubu a Arewa? Gaskiya ta fito
Primate Ayodele ya ce ya hango shugabannin kasashe wadanda suka kwashe lokaci a kan mulki, suna cikin hadarin fuskantar hakan.
Ya yi kira musamman ga shugabannin kasashen Côte d’Ivoire da Kamaru, wadanda suka shafe shekaru sama da 10 a kan karagar mulki, da su yi taka-tsantsan.
"Na hango shugaban wata kasa a Afrika zai iya fadawa tarkon yin garkuwa da shi. Ban san yadda zai faru ba, amma na ga wasu sojoji na musamman suna yi wa shugabannin kasashen da suka daɗe a mulki barazana."
"Dole ne shugabannin kasashen Cote d'Ivoire da Kamaru su yi taka tsan-tsan kan hakan"
- Primate Babatunde Elijah Ayodele
Malami ya hango makircin Emmanuel Macron
Hakazalika, Primate Ayodele ya yi ikirarin cewa shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron na da wani shiri da zai illata kasashen Afrika da dama.
Ya ce daga cikin kasashen har da Jamhuriyar Benin, Burkina Faso, Mali, Nijar, Burundi da Senegal, rahoton jaridar Independent ya tabbatar da labarin.
Malamin addinin ya gargadi shugabannin wadannan kasashe, da su zage damtse wajen kare kansu da kasashensu daga shirin kasashen Yammacin duniya na sake maida Afrika tamkar mallakarsu.

Source: Twitter
"Macron na da wani shiri da zai lalata kasashe da dama a Afrika, dole shugabannin Benin, Burkina Faso, Mali, Nijar, Burundi da Senegal su kula."
"Ana son a sake bautar da Afrika, dole ne shugabannin kasashe su zage damtse don kare nahiyar daga fadawa hannun Turawan Yamma."
- Primate Babatunde Elijah Ayodele
Wannan sabon hasashen na Primage Ayodele na zuwa ne bayan wani gargadi da ya taba yi cewa nan da shekaru 20 masu zuwa matasa za su tayar da wata gagarumar guguwa ta juyin-juya hali a fadin nahiyar Afrika.
Ayodele ya yi hasashe kan tazarcen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban malamin addinin Kirista, Babatunde Elijah Ayodele, ya yi hasashe kan tazarcen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2027.
Primate Ayodele ya ja kunnen Shugaba Tinubu kan cewa akwai wasu mutane uku da za su iya kifar da shi.
Malamin addinin ya bayyana cewa daga cikin wahayin da aka yi masa na mutanen da za su iya kayar da Tinubu, babu tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathana cikinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
