Rikici Ya Barke a Wurin Taron Sarakuna da Aka Nemi Gwamna Ya Tsige Sarki a Najeriya

Rikici Ya Barke a Wurin Taron Sarakuna da Aka Nemi Gwamna Ya Tsige Sarki a Najeriya

  • Rikici ya barke a yunkurin tsige Sarkin Ipetumodu, wanda kotun kasar Amurka ta daure tsawon watanni 56 a gidan yari
  • A wani taro da aka shirya a masarautar Sarkin da ke jihar Osun, masu nadin Sarki da 'yan gidan sarauta sun tashi baram-baram
  • Wannan lamari dai na zuwa ne bayan kira ga Gwamnan Osun ya sauke Sarkin saboda hukuncin da kotun Amurka ta yanke masa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Rikici ya barke tsakanin 'ya'yan gidan sarauta na masarautar Ipetumodu a wurin wani taron da suka gudanar a jihar Osun.

Hakan dai na zuwa ne bayan kiran da aka yi ga Gwamna Ademola Adeleke da ya tsige Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede saboda hukuncin da aka yanke masa a Amurka.

Oba Oloyede.
Hoton Sarkin da aka daure a kasar Amurka, Oba Oloyede Hoto: Bright Sunday
Source: Twitter

Punch ta tattaro a makonnin da suka shige ne aka yanke wa Oba Oloyede, wanda shi ne Apetumodu na 27 a masarautar Ipetumodu hukuncin daurin shekaru sama da hudu a gidan yari a Amurka.

Kara karanta wannan

Ambaliya ta kashe rayuka a Zariya, ruwa ya tafi da wasu mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun Amurka ta yanke masa wannan hukunci ne kan kama shi da laifin cinye kudin tallafin COVID-19 da ya karba ta hanyar amfani da bayanan karya.

Rikici ya barke a taron sarakuna a Osun

Wannan ya sa masu zaben Sarki da sauran 'yayan gidan sarautar suka fara tarurruka da nufin tattaunawa kan makomar Sarkin don daukar matakin da ya dace

An ruwaito cewa sarakunan yankin sun kira wani taro, wanda aka gudanar a fadar masarautar karkashin jagorancin Asalu na Ipetumodu, Cif Sunday Adedeji.

Bayanai sun nuna cewa an fara taron da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin jiya Talata ba tare da wata matsala ba, har sai da wani ɗan gidan sarauta ya nemi a rubuta wasika a hukumance zuwa ga Gwamna Adeleke.

An fara neman gwamnan Osun ya tsige Sarki

Ya bukaci Adedeji, wanda shi ne shugaban masu nadin sarki, da ya rubuta takarda zuwa ga Gwamna Adeleke domin neman ya ayyana kujerar sarkin da babu kowa a kanta.

Kara karanta wannan

Taron maulidin Annabi SAW ya hargitse, an kama mutane 30 dauke da makamai

Sai dai Adedeji ya ki amincewa da wannan bukata, inda ya sanar da cewa ba zai shiga cikin irin wannan yunkuri ba.

Wannan ne ya tayar da ce-ce-ku-ce da hayaniya tsakanin mahalarta taron, abin da ya sa taron ya tarwatse da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, in ji rahoton PM News.

Gwamna Adeleke na jihar Osun.
Hoton Gwamna Ademola Adeleke a taron gwamnonin PDP da aka yi a Zamfara, da Oba Oloyede
Source: Facebook

Wace matsala aka cimma a taron masarauta?

Bayan taron, wani ɗan sarauta daga gidan Aribile, Olaboye Ayoola, ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda Adedeji ya ƙi amincewa da matsayar da aka cimma a taron.

“Mun cimma matsaya cewa a zabi sababbin masu nada Sarki guda biyu domin maye gurbin waɗanda suka rasu sannan a rubuta takarda zuwa ga gwamna, a nemi ya tsige Sarki," in ji shi.

Amma Cif Adedeji ya ƙi amincewa, sannan ya sanar da cewa ba shi da sha’awar ci gaba da zama mai nada sarauta, "wannan ya jawo rikici, taron ya tarwatse ba tare da cimma matsaya ba.”

Da aka tuntube shi, Adedeji ya tabbatar da ƙin amincewarsa da wannan bukata, inda kawai ya ce: “Eh, gaskiya ne. Amma dole zaman lafiya ya tabbata da farko.”

Kara karanta wannan

"Mun gano tushen matsalar": Gwamna Uba Sani ya fadi dalilin sulhu da 'yan bindiga

Gwamna Adeleke na tunanin tsige Sarki

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun na duba yiwuwar tsige Mai Martaba Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede.

Hakan dai na zuwa ne bayan kotun Amurka ta yanke wa sarkin hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni 56.

Rahotanni sun nuna cewa matukar ba a samu wani sauyi daga baya ba,.Gwamna Adeleke zai tube wa Sarkin rawani sakamakon laifin da ya aikata a Amurka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262