Ambaliya Ta Kashe Rayuka a Zariya, Ruwa Ya Tafi da Wasu Mutane

Ambaliya Ta Kashe Rayuka a Zariya, Ruwa Ya Tafi da Wasu Mutane

  • Mutane uku sun mutu yayin da aka rasa wasu biyu sakamakon ambaliyar ruwa da ta biyo bayan ruwan sama a Zariya, jihar Kaduna
  • An gano gawar Fatima Sani Danmarke da wani dalibi Yusuf Surajo Tudun Wada, yayin da ake cigaba da neman wata yarinya ‘yar shekara uku
  • Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ruwan ta tafi da wani mazaunin unguwar Tudun Jukun da ya yi yunkurin ceto Fatima da ‘yar uwarta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Akalla mutane uku sun mutu, yayin da aka rasa wasu biyu sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a yankin Tudun Jukun, karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin bayan ruwan sama mai yawa da aka samu a yankin.

Kara karanta wannan

'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina

Yadda ake kokarin ceto mutane yayin ambaliya
Yadda ake kokarin ceto mutane yayin wata ambaliya. Hoto: Getty Images
Source: Original

Daily Trust ta rahoto cewa an gano gawar Fatima Sani Danmarke mai shekaru 18 da wani dalibi mai suna Yusuf Surajo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa wadanda abin ya rutsa da su sun fada cikin magudanan ruwa yayin da suke kokarin ketarawa.

Yadda aka yi ambaliya a gari Zariya

Rahotanni sun nuna cewa Fatima, wacce ke dauke da kanwarta Haneefa a baya, ta fito daga gidan kakarsu a Magume zuwa Tudun Jukun inda iyayensu ke zaune.

A lokacin ne kuma suka hadu da malamin makarantar Islamiyya, Malam Daddy, kuma ya dauke su a babur dinsa domin ya rage musu hanya.

Sai dai a yayin da suke tsallaka hanya, babur din ya kusa faduwa a cikin rafi, Fatima ta yi yunkurin tsallakawa da kanwarta amma ta zame cikin ruwan, inda ambaliyar ta tafi da su.

Ruwa ya tafi da wani mutum a Zariya

Wani mazaunin Tudun Jukun, Mustapha Badamasi Dan Bakano, ya ce wani mutum ya yi kokarin tsalle cikin ruwan domin ceto Fatima da kanwarta, amma shi ma ruwa ya yi awon gaba da shi.

Kara karanta wannan

Wike ya laftawa Ganduje da wasu manya tarar miliyoyin Naira a kan filaye

Rahoton Aminiya ya tabbatar da cewa an gano cewa ya mutu daga baya kuma an yi masa jana'iza da safe a unguwar Gidan Dangoma.

Haka kuma, an gano gawar Yusuf Surajo, wanda aka fi sani da Abba, a karkashin gada kusa da makarantar firamare ta Isan Nabawa, Tudun Wada.

Gwamnan jihar Kaduna na bayani a wani taro
Gwamnan jihar Kaduna na bayani a wani taro. Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Ruwa ya tafi da wata daliba a Zariya

A wani lamari daban a Tudun Jukun, ambaliya ta tafi da daliba mai suna Zainab Abdulkadir, kuma duk da yunkurin masu iyo, ba a iya ceto ta ba, kuma har yanzu ba a gano ta ba.

Hukumar NEMA da gwamnatin tarayya sun sha gargadin al'umma kan zama cikin shiri domin kaucewa fadawa hadarin ambaliya a daminar bana.

Ruwa ya yi gyara a jihar Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa mamakon ruwan sama ya raba daruruwan mutane da gidajensu a jihar Kaduna.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ba bayyana cewa kimanin gidaje 171 suka rushe bayan shafe kwaki ana zagba ruwan.

Yayin da ake cigaba da tallafawa wadanda ambaliyar ta shafa, wani rahoto ya bayyana cewa sama da mutum 500 ne suka rasa wajen zama.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng