'Yan Ta'adda Sun Badda Kama yayin Tafka Ta'asa a Zamfara

'Yan Ta'adda Sun Badda Kama yayin Tafka Ta'asa a Zamfara

  • 'Yan ta'adda sun zo da sabon salo wajen tafka ta'asa kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Zamfara
  • Tantiran 'yan ta'addan sun yi basaja inda suka tasa keyar wasu mutane zuwa cikin daji a karamar hukumar Maru
  • Jami'an tsaron sun bi sawunsu inda suka yi kacibus da irin kayayyakin da suka yi amfani da su wajen badda kama don ka da a gano su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki a garin Dansadau, da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

A yayin harin da 'yan ta'addan su ka kai, sun yi awon gaba da mutane takwas wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

'Yan ta'adda sun badda kama wajen sace mutane a Sokoto
Hoton Gwamna Dauda Lawal, sanye da kayan rundunar Askarawan Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Harin 'Yan Boko Haram ya fusata sojoji, sun hallaka tsageru masu yawa a Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan ta'adda sun kai hari a Zamfara

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa harin ya faru ne a wajen garin, da safiyar ranar Lahadi, 7 ga watan Satumba, lokacin da wasu mutane ke tsaka da barci.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun shigo cikin garin da wani sabon salo, inda suka sanya hijabai domin su boye ainihin kansu da kuma kaucewa gano su.

Bayan sun kutsa cikin garin, sai su ka yi garkuwa da mutane takwas, sannan suka tsere cikin daji.

Sojoji sun gano kayan 'yan ta'adda

Majiyoyi sun ce bayan samun labarin harin, dakarun soji tare da yan sa-kai sun bi sawun ‘yan ta’addan, amma ba su yi nasarar samun su ba.

Duk da haka, an gano wata jakar kaya da suka bari yayin guduwa da ta kunshi hijabai da rigunan mama da suka yi amfani da su wajen badda kama.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama 'yan bindigan da suka kai hari masallaci ana sallar asuba

Wannan ya zama hujja ta yadda suka aiwatar da wannan mummunan shiri.

"Dakarun sojoji tare da hadin gwiwar 'yan sa-kai sun bi sawun 'yan ta'addan amma ba su tarar da su ba."
"An gano wata jaka dauke da hijabai da rigunan mama da 'yan ta'addan suka yi amfani da su."

- Wata majiya

Harin ya sake jefa al’ummar yankin cikin tsoro da damuwa, musamman ganin yadda masu garkuwa da mutane ke kara kirkirar sabbin dabaru na aikata miyagun laifuffuka.

'Yan ta'adda sun sace mutane a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan 'yan ta'adda

Dakarun sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram

A wani labarin kuma, jun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun kai hare-hare ne ta sama da kasa kan 'yan ta'addan bayan sun hallaka mutane 63 a karamar hukumar Bama.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun yi dirar mikiya a kan mazauna Zamfara, sun kashe mutane

Hare-haren sun yi sanadiyyar kashe mayaka da kwamandoji kungiyar, inda majiyoyi su ka ce an binne gawarwakin kusan mutum 50.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng