Wike Ya Laftawa Ganduje da Wasu Manya Tarar Miliyoyin Naira a kan Filaye

Wike Ya Laftawa Ganduje da Wasu Manya Tarar Miliyoyin Naira a kan Filaye

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya aza tarar N5m ga manyan mutane ciki har da Abdullahi Ganduje bisa laifin sauya filaye ba tare da izini ba
  • Rahotanni sun nuna cewa an ba masu filayen kwanaki 30 su biya tarar ko su fuskanci ƙarin matakai daga hukumar birnin tarayya Abuja
  • Bayan haka, za a fitar da sababbin takardun mallaka bayan an biya tara tare da sabunta amfani da filayen na tsawon shekara 99 masu zuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (Abuja), Nyesom Wike, ya aza tarar Naira miliyan 5 ga manyan mutane a Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa an ci tarar mutanen ne bisa laifin sauya amfani da filaye ba tare da samun izinin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama 'yan bindigan da suka kai hari masallaci ana sallar asuba

Wike yana magana da Abdullahi Ganduje a kwanakin baya
Wike yana magana da Abdullahi Ganduje a kwanakin baya. Hoto: APC Nigeria
Source: Facebook

Rahoton Arise News ya ce matakin ya haɗa da gidaje da filayen wasu tsofaffin manyan jami’an gwamnati, alƙalai, hafsoshin soja, da kuma hukumomin gwamnati da masu zaman kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya bayyana cewa dole ne waɗanda abin ya shafa su biya tarar nan da kwana 30 domin gujewa ƙarin hukunci daga gwamnati.

Ganduje da sauran wadanda tarara ta shafa

Rahotanni sun nuna cewa Ganduje ya sauya wani gida da aka amince da shi a matsayin wurin zama a Wuse 2, zuwa wajen hada-hadar kudi, wato banki.

Haka kuma, an sauya wani gida a Maitama da ya kasance mallakin tsohon babban hafsan soja a lokacin mulkin Babangida, marigayi Janar Tunde Idiagbon zuwa otal.

Bugu da ƙari, tsofaffin alkalan kotun koli biyu, Mai Shari’a Atanda Fatai-Williams da Mai Shari’a Aloma Mariam Mukhtar, suma sun shiga jerin waɗanda aka ci tarar.

An sauya gidan Fatai-Williams zuwa masana’antar katako da shago mai hawa biyu, yayin da gidan Mukhtar da aka amince da shi a matsayin wurin zama aka mayar da shi shago.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Bako daga kasar waje ya yi mutuwar da ba a yi tsammani ba a Abuja

Karin wadandda Wike ya ci tarar su

Wike ya ce Sanata Shehu Sani ya sauya gidansa a Aminu Kano Crescent zuwa wajen tallata kaya, haka ma tsohon jami'in kungiyar gwamnoni, Okauru Okauru ya aikata irin laifin.

Tsohon hafsan soja, Laftanar Janar Rufus Kupolati, ya mayar da gidansa wajen motsa jiki, yayin da tsohon ministan Abuja, Abba Gana, ya maida gidansa zuwa katafaren shago ba tare da izini ba.

Haka kuma, an ce Kamfanin NNPC ya mayar da gininsa zuwa cibiyar lafiya, yayin da hukumar ‘yan sanda ta sauya wani fili da aka ware mata zuwa ginin kungiyarsu ta POWA.

Wike yayin da ya ke wan bayani a Abuja
Wike yayin da ya ke wan bayani a Abuja. Hoto: Nyesom Ezonwo Wike
Source: Facebook

Bayanin da Wike ya yi kan lamarin

A cewar Wike, wannan hukunci ya shafi gidaje da filaye da ke manyan tituna a Maitama, Asokoro, Wuse 2, Garki 1 da Garki 2.

Rahoton This Day ya nuna cewa Wike ya jaddada cewa wannan mataki zai zama izina ga sauran masu filaye su daina karkatar da su ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

'Abubuwa 4 ne ke rura wutar ta'addanci,' Gwamna Uba Sani ya nemo mafita ga Arewa

Wike ya yi wa Tambuwal martani

A wani rahoton, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi magana kan abubuwan da Aminu Tambuwal ya fada a kansa.

Wike da ya yi magana ta bakin hadiminsa ya bayyana cewa ya saurari abin da Tambuwal ya fada kuma zai mayar da cikakkiyar amsa nan gaba.

A makon da ya wuce ne Aminu Tambuwal ya yi maganganu a kan Wike game da siyasa a wata hirar da aka yi da shi a Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng