Dubu Ta Cika: An Kama 'Yan Bindigan da Suka kai Hari Masallaci Ana Sallar Asuba

Dubu Ta Cika: An Kama 'Yan Bindigan da Suka kai Hari Masallaci Ana Sallar Asuba

  • Rahotanni sun nuna cewa masu ibada uku sun shiga hannun ‘yan bindiga yayin sallar Asuba a Dansadau, Zamfara
  • Biyo bayan lamarin, jami’an tsaro sun cafke mutum shida da ake zargi da hannu cikin harin da ya faru a masallaci
  • Sojojin Najeriya sun kai hare-haren sama da ƙasa a Sambisa da Mandara, sun hallaka mayakan ISWAP da Boko Haram

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da mutane yayin da suka kai hari da Asuba.

Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne yayin da ake sallar Asuba a yankin Maru, jihar Zamfara, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin tashin hankali.

Taswirar jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka kai harin ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun yi dirar mikiya a kan mazauna Zamfara, sun kashe mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace mutane a masallacin Zamfara

Maharan sun kutsa cikin wani masallaci da ke unguwar Yarlaluka, a garin Dansadau, inda suka yi garkuwa da wani mai suna Alhaji Garba Akarya da wasu mutum biyu.

Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun isa wurin inda suka cafke mutane shida da ake kyautata zaton suna da nasaba da harin.

Bayan kama su, rahotanni sun nuna cewa yanzu haka jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike a kansu.

Harin 'yan bindigan ya girgiza yankin Dansadau

Harin da ya faru da misalin ƙarfe 5:55 na safe ya ƙara jaddada barazanar tsaro da al’ummar yankin Dansadau ke fuskanta.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shigo da bindigogi cikin masallacin da ke cike da masu ibada, inda suka yi dirar mikiya suka firgita jama'a.

Jihar Zamfara na cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalolin 'yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

'Abubuwa 4 ne ke rura wutar ta'addanci,' Gwamna Uba Sani ya nemo mafita ga Arewa

Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram

A wani labarin tsaro na dabam, dakarun Najeriya sun kai mummunan farmaki kan mayakan ISWAP da Boko Haram a cikin dajin Sambisa da tsaunukan Mandara.

Wannan ya biyo bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai ƙauyen Darajamal a Bama, jihar Borno, inda suka hallaka mutane 60.

Sojojin sama na Operation Hadin Kai tare da tallafin dakarun ƙasa ne suka kaddamar da hare-haren da suka lalata sansanonin mayakan.

Wasu sojojin Najeriya a bakin aiki
Wasu sojojin Najeriya a bakin aiki. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Depositphotos

Wani mazaunin yankin ya ce ‘yan ta’addan sun shigo da yammacin Juma’a suna harbi ba kakkautawa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar jama’a da dama.

Sai dai bayan tserewarsu, sojojin Najeriya sun bi sawunsu ta hanyar dabarun sa ido na sama tare da kai hare-hare masu ƙarfi.

An yi sulhu da 'yan bindiga a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da yin sulhu da 'yan bindiga da aka yi fama da su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an samu asarar rayuka

Rahotanni sun bayyana cewa an yi sulhun ne a Birnin Gwari domin kawo karshen zubar da jini a yankin bayan shafe shekaru ana kashe mutane.

Sakamakon sulhun da aka yi, tubabbun 'yan bindiga sun samu damar shiga kasuwa domin sayayya da kuma asibitin Birnin Gwari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng