Jerin Lokutan da Shugaba Tinubu Ya Tafi Hutu Kasashen Waje cikin Shekara 2

Jerin Lokutan da Shugaba Tinubu Ya Tafi Hutu Kasashen Waje cikin Shekara 2

FCT, Abuja - Yawan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da Shugaba Bola Tinubu ke yi, musamman waɗanda ake kira “hutu tare da aiki”, sun jawo magana a shafukan sada zumunta.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, Tinubu ya yi tafiye-tafiye da dama zuwa kasashen waje domin diflomasiyya da harkokin tattalin arziki.

Shugaba Tinubu ya je hutu a kasashen waje
Hoton shugaban kasa Bola Tinubu yana dago hannu kafin shiga jirgin sama Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Bola Tinubu na zuwa hutu kasashen waje

Binciken da jaridar Tribune ta gudanar ya nuna cewa, tun bayan hawa mulki, Tinubu ya je kasashen waje akalla sau biyar cikin shekara biyu don abin da ake kira “hutu tare da aiki”.

A wasu lokutan kuma, Shugaba Tinubu ya kan yada zango a wasu kasashen don hutawa bayan ya dawo daga ziyarar aiki.

1. Hutu a birnin Landan, Birtaniya

Bayan halartar taron New Global Financial Pact Summit a birnin Paris, Faransa (22–23 ga Yuni, 2023), Tinubu ya tafi Landan domin yin gajeren hutu kafin komawa Najeriya don shagulgulan Sallah.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga ke karbar haraji har N500,000 kafin a birne mamaci a kabari

Jaridar Nairametrics ta ce tun da farko an tsara Shugaba Tinubu zai dawo gida ne a ranar 24 ga watan Yunin 2023.

Wannan ana kallonsa a matsayin hutu bayan kammala ziyara.

2. Hutu tare da aiki a Birtaniya da Faransa

A ranar 2 ga watan Oktoba, 2023, Tinubu ya bar Abuja zuwa Birtaniya domin hutun makonni biyu da aka bayyana a matsayin ɓangare na hutun shekara, domin yin nazari kan gyare-gyaren tattalin arziki.

A ranar 11 ga watan Oktoba, Shugaba Tinubu ya bar Birtaniya zuwa birnin Paris, Faransa, domin wani “muhimmin al’amari” wanda wasu majiyoyi suka ce ya haɗa da lokaci na kashin kansa ko kuma zuwa duba lafiya.

3. Ziyarar sirri zuwa Faransa

Jaridar TheCable ta kawo rahoto cewa a ranar 24 ga watan Janairu, 2024, Shugaba Tinubu ya tafi Faransa domin wata ziyara ta sirri, sannan ya dawo ranar 7 ga watan Fabrairu, 2024.

Fadar shugaban kasa ba ta bayyana cikakkun bayanai kan tafiyar ba, amma masu suka ciki har da Atiku Abubakar sun ce hutu ne, inda suka kalubalance ta la’akari da kalubalen da ake fuskanta a cikin gida.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya tafi hutun shekarar 2025, ya lula zuwa kasashe 2 a nahiyar Turai

Wasu majiyoyi sun ce wannan tafiya ta iya haɗawa da ganin likitoci, abin da aka riga aka saba tun kafin hawansa mulki.

4. Yada zangon Tinubu a Faransa

Bayan ziyarar aiki zuwa kasar Netherlands (23–27 ga watan Afrilu, 2024) da kasar Saudi Arabia (28–29 ga watan Afrilu, 2024) domin taron World Economic Forum, Tinubu ya kara yin wasu kwanaki a nahiyar Turai.

Shugaba Tinubu ya sauka ne a kasar Faransa, kafin dawowa gida Najeriya a ranar 8 ga watan Mayu, 2024.

Ana ɗaukar wannan a matsayin lokacin kashin kansa, ko da yake ba a bayyana shi a hukumance a matsayin hutu ba. Ya dai kwashe jimillar kwanaki biyar zuwa bakwai.

5. Shugaban kasa ya tsaya a Birtaniya

Bayan halartar taron hadin guiwar Sin da kasashen Afrika a Beijing (29 ga Agusta – 6 ga Satumba, 2024), Tinubu ya shafe kwanaki bakwai a Birtaniya kafin dawowa Najeriya a ranar 14 ga Satumba, 2024.

An bayyana wannan a matsayin lokacin kashin kansa, watakila wani ɓangare na hutun shekara.

6. Hutu tare da aiki a Birtaniya da Faransa

Kara karanta wannan

Farashin Dala: Bincike ya karyata ikirarin Tinubu kan farfado da darajar Naira

A ranar 2 ga watan Oktoba, 2024, Tinubu ya tafi hutun makonni biyu a Birtaniya domin yin nazari kan gyare-gyaren da yake aiwatarwa.

Tashar Channels tv ta ce ya tsawaita wannan tafiya zuwa birnin Paris, Faransa, sannan ya dawo Najeriya a ranar 19 ga Oktoba, 2024.

Fadar shugaban masa ta bayyana tafiyar a matsayin wani ɓangare na hutun shekara, duk da cewa masu suka sun ce hakan ba dace ba duba yanayin kalubalen da ake fuskanta a cikin gida ba.

Shugaba Tinubu ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje
Hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana saukowa daga jirgin sama Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

7. Hutu da aiki a Faransa da Birtaniya

A ranar 4 ga watan Satumba, 2025, Shugaba Tinubu ya tafi hutun kwanaki 10 zuwa kasashen Faransa da Birtaniya, wanda aka bayyana a matsayin ɓangare na hutun shekara.

Fadar shugaban kasa cikin wata sanarwa a shafin X ta ce zai raba lokacin nasa tsakanin kasashen biyu, ba tare da bayyana wani takamaiman bayani kan harkokin da zai yi ba.

Shugaba Tinubu ya kori hadiminsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sallami daya daga cikin hadimansa, wanda yake aiki aiki a ofishin Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

"Babu wani makirci": Kwankwaso ya yi magana kan tazarcen Tinubu a 2027

Shugaba Tinubu ya kori Fegho John Umunubo, wanda yake taimakawa mataimakin shugaban kasa kan harkokin tattalin arzikin zamani da kirkire-kirkire.

A cikin sanarwar korar da aka yi wa hadimin shugaban kasan, an gargadi masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arzikin zamani da.kirkire-kirkire, da su guji yin mu'amala da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng