Mamakon Ruwa Ya Rikito da Gini a kan Bayin Allah a Jigawa, An Rasa Rai
- Ruwan sama mai karfi da aka shafe kwanaki biyu ana yi a jihar Jigawa ya rushe wani gini da ake tunanin ya tsufa sosai
- Gwamnatin ƙaramar hukumar Kirikasamma ta bayar da tallafin kuɗi ga waɗanda abin ya shafa a Jigawa
- Ana kira ga gwamnati da kungiyoyi masu taimako su tallafa wa al’umma kan masifar ambaliyar ruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa – Mamakon ruwan sama da aka shafe kwanaki biyu ana yi ya kayar da wani gini a jihar Jigawa.
Rahotanni sun bayyana cewa mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon rushewar wani gini.

Source: Twitter
Tashar TVC ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Kabak da ke ƙaramar hukumar Kirikasamma, a Jigawa.

Kara karanta wannan
Tinubu zai kawo tsarin aiki da ba a taba yi ba a Najeriya, komai zai sauya a ofisoshi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gini ya fadi a kauyen jihar Jigawa
The Cable ta wallafa cewa ginin ya tsufa sosai, kuma ya fadi bayan ruwan ya kara rubar da ginshikan gidan, wanda ya sa su ka yi laushi sosai.
Waɗanda suka jikkata na ci gaba da samun kulawa a asibiti, yayin da aka sallami wasu biyu daga cikinsu.
Hukumomi sun ce za a ci gaba da lura da lafiyar waɗanda ke asibiti domin tabbatar da cikakken sauƙi.

Source: Twitter
Shugaban ƙaramar hukumar Kirikasamma, Muhammad Maji Wakili Marma, ya bayyana wannan al’amari a matsayin abin takaici da girgiza zuciya.
Ya ziyarci iyalan wadanda lamarin ya shafa domin jajanta masu da nuna goyon bayan gwamnatin jihar Jigawa.
Gwanmnatin Jigawa ta taimakawa jama'a
Shugaban ƙaramar hukumar ya sanar da bayar da ₦500,000 domin kula da lafiyar waɗanda suka jikkata.
Sannan ya sanar da bayar da ₦100,000 ga iyalan mamacin a matsayin tallafin gaggawa gare su.
Ya yi kira ga gwamnatin jiha da ƙasa, tare da kungiyoyin agaji da su kawo ɗauki cikin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.
Ya ce:
“Idan ba a dauki matakin gaggawa ba, akwai yiwuwar wasu gidaje su rushe saboda tsananin ruwan sama da muke fama da shi. Wannan na iya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi fiye da haka.'
Jihar Jigawa na daya daga cikin jihohin Arewa da ke fama da ambaliya a kowace shekara, lamarin da ke haddasa rushewar gidaje da lalata gonaki.
Jigawa na daga cikin jihohin Najeriya 14 da gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa za ta fuskanci mamakn ruwa kamar da bakin kwarya a cikin kwanakin nan.
An samu hadarin kwale-kwale a Jigawa
A baya, mun ruwaito cewa hatsarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mutane shida, yayin da har yanzu aka rika neman wasu biyu a Jigawa.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar hatsarin jirgin ruwan na gargajiya a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, 29 ga watan Yuli, 2025.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 27 ga Yuli, 2025, lokacin da kwale-kwale da ke dauke da yara 15 daga gonar Jejin Gunka zuwa ƙauyensu ya kife a ruwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
